Matsalar Tsaro: Bincikena Ya Gano Hanyoyin Da Za a Bi Don Kai Karshen Matsalar Tsaro---Dakta Murtala Ahmad

Wani abu da yafi ciwa da dama daga 'yan Najeriya tuwo a kwarya a Wannan lokaci bai wuce, matsalar tsaro ba, matsalar da ta zama sanadin rasa rayukan yan kasa da dama baya ga jikkatawa dama raba daruruwa da muhallan su. Jami'o'i dai sun kasance cibiyoyin gudanar da bincike-bincike, to amma ba kasafai ake samun manazarta dake mayar da hankali kan matsalar nan ta tsaro. A jami'ar Usmanu Danfodiyo dake Sokoto wani malamin tarihi Dokta Murtala Ahmad Rufai ya shafe shekaru 10 yana gudanar da bincike kan matsalar tsaron arewacin Najeriya musamman ma dai jihar Zamfara, sakamakon binciken da aka gabatar a jami'ar kuma aka yiwa take da "I am a Bandit" ma'ana ni dan bindiga ne. Aminu Amanawa ya tattauna da malamin kan binciken nasa in da ya fede biri har wutsiya kan matsalar tsaron.

Matsalar Tsaro: Bincikena Ya Gano Hanyoyin Da Za a Bi Don Kai Karshen Matsalar Tsaro---Dakta Murtala Ahmad
 

 

Dakta Murtala Ahmad Rufa'i ka yi mana bayani kan binciken nan da ka shafe shekaru goma kana gudanarwa a kan ita wannan matsalar ta tsaro?

 

A'uzubillahi minashaitanin rajin, Bisimillahir rahmanin raheem,  masu karatu Ni sunana Murtala Ahmed Rufa'i kuma ni dalibin tarihi ne, kuma abinda na yi tayi a rayuwata ina kokari in karanci Tarihi in tattara bayanai daga mutanen da abun da ya shafa, na fara wannan binciken shekara kusan goma da suka gabata, tun matsalar na karama ba'a santa ba, babu wanda ya kula da'ita, babu wanda ya maida hankali gare ta na fara kokarin soma gudanar da bincike a kanta, ba cikin jahar Zamfara kawai ba kusan na yi bincike a Sakkwato na yi shi a Kebbi na yi shi a Katsina na yi shi a Neja na yi shi a Kaduna, duka a kan matsalolin nan na tsaro, kuma abin da ya jawo ra'ayina ba shi ne fannina na karatu ba, ni mutum ne dana tashi ina karatun sana'a ta sakai, ma'ana saye da sayarwa na abinci, kuma saye da sayarwa na abincin nan abune wanda ya bukaci dole ne mutum ya je kasuwanni, kasuwanni bana birane ba kasuwanni na karkara, saboda mafi yawancinsu sana'a sakai misali sana'a ce wacce a keyi a karkara, to a lokacin da ni ke wannan binciken nawa na sana'a na abinci da a ke cewa sakai a lokacin wannan matsalar ta kunno kai ina cikin kasuwa ina hira da mutane masu sayen abinci da masu sayarwa mata da maza na kanji mutane na ambatar sun fara samun wata sabuwar matsala da ta bullo ga abinda ke faruwa ga abinda ke faruwa, ana magana an fara daukar shanu an daya, an dauki biyu, abinda matsala ce wacce a babbar matsala to kusan duk kasuwar da naje Allah da ikonai zan taradda da wannan matsalar saboda mutane ne daga bangarori daban-daban daga fanni daban-daban suka zo kasuwanin nan, kuma idan a kazo kasuwa daman ai ba siye da sayarwa kawai a ke yi ba, ana bada labari kuma ana tattauna abubuwan dana shafi ko wane gari da kowanne yanki da kuma ko wanne bangare, kamar wata majalisa ce ta yada bayanai ta samun bayanai da kuma yadata.

To a hakikanin gaskiya ko da na ke batun kare wannan karatun na sakai na fara tattara bayanai ina da hulda da mutane matuka, wadannan mutanen Allah da iko nai akwai wadanda ya zamanto cewa da bala'in ya yi bala'i sun dauki bindiga sun dauki makamai sun shiga daji.

 
Cikin wadan da kuke hulda da su?
 
Wadanda muke huldanya da su na saye da sayarwa na abinci nan, ina da numbobin su don duk lokacin da na je na yi hira da su na kare hira da kai zan dauki sunanka, zan dauki shekarun ka, zan dauki sunan garinku sa'annan zan karbi number wayarka, ma'ana ko da Allah ya kaddari na dawo Sakkwato makaranta kila ina bukatar karin bayani ba sai  na sake komawa gare ka ba zan iya kiranka in samu bayani.
To yanzu haka littafin da nayyi wannan yawace yawacen idan ka duba littafine wanda ya ke dauke da sunayen mutane da lambobin wayoyinsu, kuma Allah da iko nai ya kaddari mutanan nan da suka shiga daji anzo an yi rikici shekara uku shekara hudu sun dauki makamai sun jikkita duk wanda suke son su jikkita, sun saci shanu sun saci duk abinda suke su yi, Allah da iko nai ya kaddari gwamnatoci sun yafe musu kuma sun zamo tubabbu, duk lokacin da naji ance za'ayi taro na yan bindiga ko kuma yafewa yan bindiga kona sulhu misali na kanyi kokari inje kuma Allah ya kaddari duk naje bazan rasa mutum biyu mutum uku mutum hudu ba, idan na fara magana za su tambayeni a'a Malam kana nan?, lallai ina nan, ya kaza ya aiki? ya kwana biyu ya kaza?, wasu basu ganeni nima zan nuna masu ai nine wani dana iske ka rana kaza kasuwa kaza muka tattauna ka iya tuna yaron dalibinan mai karatun sakai?, sai ya ce "eh lallai Murtala ne?", Sai ince eh lallai Murtala ne, to kaji dalilin inda huldar ta taso, tunda an yadda dani an amincemin kamin a shiga aikin nan na yan bindiga, tabbas wasu daga cikinsu dana hadu dasu sun yadda dani sun amincemin dukka bayanai na sirri na rayuwarsu cikin dajin nan, makamansu yadda suka samesu yadda suke amfani dasu yadda a ka yi suka shiga ciki da kuma abinda ya sa suka baro wannan sana'a ta bindiga kusan ba mutum guda ahadun wanda ya boyemin.
 
Tau da ya ke ka yi hulɗar  dasu ka fahimci rayuwarsu takamaimai me ka gano a matsayin musabbabin da ke jefa da dama daga cikinsu ayukkan nan da suke?
 
Malam Aminu tsakanin da Allah babu abinda yasa su cikin wannan hali illa sake da kuma tabarbarewar tsaro wanda ke da hannun shuwagabanni, tsakani da Allah ba a cewa sun dauki Bindiga saboda talauci amma gwamnatoci sun yi sa ke dan zaki ya girma, saboda mi? Abin nan tun yana farko ya kamata a ce an tashi tsaye tsayin da ka , misali Malam Aminu ankai karshen shi, amma babu ruwan kowa, abubuwan da ka faruwa kauyukka Malam Aminu babu ruwan kowa bubu ruwan hukuma babu ruwan Gwamnati, Sarakuna na gargajiya Alal misali masu hakimai da masu anguwanni, duk taro da a kai za kaji suna magana, sufa kasassu babu lafiya, tun wannan lokacin ina yima maganar shekara bakwai shekara takwas da suka wuce , alil dubu biyu da goma sha biyu misali (2012) Ni Murtala na je Adama anyi yaki da a ke cewa dan adama, yakin dan Adaman nan babu yankin da mutane basu zo suka halacci wannan yakin ba.
 
A wace jaha kenan?
 
Anan jahar Sakkwato a ka yi ta bangaren Shinkafi da Isa da Sabon birni da sauransu, mutane sun tashi sun duki makamai anyi wajen awa uku da rabi zuwa awa hudu ana gwabzawa tsakanin barayin nan da mutanen gari, anyi na tubali Alal misali cikin yankin Mafara , sa'annan abunda yasa wannan bala'in ya shahi jahar Sakkwato baka banbanta Isa da Shinkafi, baka banbanta Bargaja da Badarawa, saboda kusancin su.
Lokacin da rikicin nan cikin Zamfara mutanen mu na Bargaja suna tashi su kaima yan uwansu da ke Badarawa da ke Shinkafi tallafi da kuma gudummawa da kuma a gaji, kakka manta yan ta'addan nan sun sani kuma suna iya babban tawa, saboda lokacin nan da nake magana ba baki bane yan gida ne, saboda haka duk wanda ya kawo gudummawa daga duk inda ya hito alal misali sun sanshi ka ji asali kaji silan abunda yasa abun nan ya shafi jihar Sakkwato.
 
Da ya ke cikin bayananka na farko ka bayyana cewa ka samu halartar irin tarukan sulhun nan da a ke da yan Bindiga wurare da dama din nan sai ya zamana duk da sulhun nan  da a ke yi dasu sau tari matsalar nan ta tsaro sai kara ta'azzara ta ke yi, kaman a binciken da ka gudanar menene musabbabin a maimakon  abun ya rika raguwa sai ma karuwa yake?
 
To a hakikanin gaskiya Aminu ni a nawa tunani da kuma hange da bibiyar abubuwan nan da nake yi tsakani da Allah ban taba sanin anyi sulhu ba, ana dai taro na yan siyasa a dauki hotuna yan jarida a fada musu abinda zasu fadama al'umma ayi a kare a watse.
 
Kaman ba a sulhun kenan?
 
In anyi sulhu ina ganin sulhun da nissan anyi wanda an kayi na gaskiya shi a sulhun da a ka yi a Zamfara 2016, lokacin mukasan anyi sulhu don sojoji suka yi wannan sulhun su suka shiga ciki suka yi ruwa sukayi tsaki, kuma sulhu ne wanda a ka yi ingantaccen sulhu saboda me? Malam Aminu mutum dubu suka kawo makami dubu ba a yi musu alkawarin allura ba kuma sunka yadda sunka bar wannan ta'addanci, kuma ina gayama mafi yawan cinsu, sun bar ta'addanci nan har yau da ake magana, saboda mi? saboda gudummawa da sojoji suka bai, sojojin nan su suka zo da idea su ta a lyi sulhu, na yi hira da wasu da a ke cewa daga Kaduna daga Sakkwato daga wasu wurare sojoji ke kiransu ta waya, kai akwai wani babban hafsan sojoji daya buga mota daga Kaduna yajje har cikin dajin Zamfara babbane wanda ya ke da iko ya murjushe mutanen nan ya aje ikonshi ya aje makananshi yazo ya zauna ya tattauna da su ya yi sulhu, wannan sulhun da yayyi misali da kuma magana da ya fada masu mai dadi da shawarwarin da ya basu suka ce sun yadda, kuma tun a wannan lokacin da a kayi wannan sulhun ya kare, wadanda na tattauna dasu na ce Alhamdulillah da alamu anyi sulhu suka ce lallai anyi sulhu kuma sun bar wannan lalura in Allah yaso har abada, amma mu sani tabbas kul badade kul ba jima yan siyasa zasu lalata ta, to magana ta gaskiya ni anawa tunanin ba a yi sulhu ba ko guda bayan wannan sulhun da a ke yi kuma wannan sulhun ya yi tasiri, taron da muke gani a jahohin da wannan abun ya shafa tsakani da Allah taro ne na siyasa, ka kira dan bindiga ya taho cikin birni ku tarosu ku tara yan jarida ku fadi abinda kuke son a fadi ƴan jarida su fadi abun da kuke son jama'a su sani.
 
To kenan wannan na nufin wadanda ake sulhun dasu ba ainihin yan bindigan bane na zahiri ko kuma ya?
 
Yan bindiga ne na zahiri, idan ka je daji ka tattauna da mutanan nan da ake cewa anyi sulhu dasu Malam Aminu idan ka shiga daji ka iske yan uwansu da ke cikin daji ka ce ina Bello za a ce Bello ya je hutu ma'ana ya karbi sulhu ya koma birni zai huta bayan kwana biyu zai dawo, alal misali ai ance anyi sulhu da Auwalun Daudawa, Auwalun Daudawa ya taho gari yayi hutu ya kare hutu nai ya koma daji, kuma ire-iren su suna nan babu adadi sunfi a kyarga, Alhaji idan za a yi sulhu a yi sulhu na gaskiya a yi sulhu na tsakani da Allah, idan kuma ba za ayi sulhu ba a bari, amma ni a tunanina da kuma nawa nazari ba ayi sulhu ba, kuma gwamnati yan siyasa basu da niyar yin sulhu, meyasa basu da niyar yin sulhu? saboda basu son wannan matsala ta kare, idan ka ji nawa ake kashewa wannan lalurar idan ka ji ko nawa suke samu da wannan matsala sai dai ka ce innalillahi wa inna ilaihirr raji'un, shiyasa ba zasu tsaya suyi sulhu na gaskiya ba.
 
Da ya ke kace ka zanta da wadannan yan bindigan kaman tunda ance talauci ne, mutanan nan suna yawan garkuwa da mutane suna neman kudin fansa, kaman a tattaunawan da ku ke yi dasu talauci zai zamo dalilin da ya sanya suke ci gaba da abun nan da suke?
 
To Malam Aminu maganar da zanyi ita ce talauci ba bakon abu bane a kasar Hausa, kuma bayani ya nuna cewa babu yadda za ayi a yaki talauci dari bisa dari a kai karshen shi,  amma abin tambaya a matsayin mu na daliban tarihi shine idan talauci ne ai akwai talauci kafin yanzu meyasa ba a yi ta'addanci ba kafin yanzu? kaga abun tambaya ne babba, mutane tabbas akwai abun tambaya ga talauci amma kuma akwai wasu abubuwa da dama da suka tattaru suka shigo cikin wannan abun, kafin yanzu na yi bayanin matsalar sulhu da ake magana, na kalubalance duka gwamnatocin nan da ke da matsalolin nan in akwai takadda guda page 1 da a ka yi signed da yan ta'addan nan na matsayin sulhu a kawo shi in gani, na yi bincike na tattauna da sauran Kwamishinoni na tsaro, na tattauna da special adviser inda a akwai su abunda na gano shine babu takkadda ko guda doddorido ne  ake yiwa al'umma.
Ga baki ake abin, kudi ake ba yan ta'addan nan su basu san ko nawa a kece a basu ba wadanda ake ba kudi basu basu abinda ya kamata su basu ba, su kuma babu wata takkada da suka sawa hannu, to ka ga magana ce kamar yadda na ce magana ce ta fatan baki, mu dai yan kallo an maishemu wawayu, jahillai anata wasa da hankalinmu da ilimin mu, batun maganar da me yaka mata ayi?, Ina nan ina aiki a kai ban kuma kare ba.
 
Baka kai ga fiddo da mafita ba kan binciken ka kenan?
 
Bankai da mafita ba, saboda wannan binciken da na ke yi jama'a ya kamata mu fahimci wani abu guda , bincikene na kamar shekara goma ba kareshi ake ba, ana cikin yinshi ne, a lokacin da duk zan fidda wannan kundin littafin da nake son in fitar alal misali a cikin wannan kundin littafin zaka ga inda ake fitar da shawarwari, sa'annan kuma akwai wadanda shawarwarin misali yafi amfani  a gare su, kai mai karatu idan an gayama ga mafita me zaka yi? ai bazaka iya yin komai ba don ba hakkin ka bane.
 
To tunda hakan ne ka taba samun dama ka zanta da masu ruwa da tsaki a lamarin tsaron nan tunda dai ana maganar ko yaushe kowa ya shigo ya ba da tashi gudummawa na magance matsalar ka taba samu ka zanta dasu a kan wannan matsalar?
 
Tabbas mun zauna kamin yanzu, mun zauna kamin in gabatar da mukala mun zauna bayan na gabatar da mukala, kuma har yanzu akwai wadanda muna waya dasu, akwai wadanda suka jinjina min kuma dana zauna da wasu daga cikinsu wallahi tallahi sai naga ashe bansan komai ba, kuma sun bani sirrin abin kamar yadda na ke ce wa matsalanan dai tamuce matsalar yan siyasa ce insun so kai karshen abun nan zasu kai karshen shi, a lokacin da suke son sukai karshen shi, wai  kaga ankai hari a gari an kashe mutane an jikkitasu gwamna dan bai tsoron Allah ya tai wa al'umma jaje wai yana kuka, wanda shi hakkin tsaro ya rataya a wuyan nai, shike kai karshen wannan abun amma yazo cikin mutane yana yi musu kuka yana tausaya musu bayan shi Allah ya bawa hakki ya, kuma abinda na ke son ka gane Malam Aminu wanda banyi bayani ba wato matsalar nan duk yadda muke tunani duk yadda muke hange duk yadda muke nazari wallahi tallahi tahi karhin tunaninmu, tunda gari za kaje ka iske rugga ko kauye misali kusan kowa ya dau makami kowa rike ya ke da makami, akwai yan ta'adda wadanda suke rike da makaman nan waranda suke aikata miyagun ayukkan ashsha, alal misali akwai wadanda aikinsu kawai shine su dauki mutane a basu kudin fansa, akwai wadanda basu da aiki illa a hita hari suje su yiwa mata fyade.
 
Kaman sun kasu kashi kashi kenan?
 
Kashi kashi, akwai wadanda dauke suke da bindiga wallahi sallar jam'i bai wuce su, karatun Alkur'ani bai wuce su, duk wani aiki na alkhiri Malam Aminu be wuce su, basu sata basu tare da mai sata kuma basu kaunar mai sata alal misali amma suna dauke da makamai , makaman nan na kariyar kansu ne da kariyar dukiyoyinsa da yan ta'addan nan da ke cikin daji, a tunani na sai anyiwa abin nan karatun ta nutsu an gano wanene ke dauke da makamai saboda ta'addanci, wanene ya ke dauke da makami ba tare da ta'addanci ba?, kuma in bincike ya nuna  aka zurfafa bincike za a gano Malam Aminu wadanda ke dauke da makaman dake cikin dajijjukkan nan don kariyar mutuncinsu, kariyar girma da darajjar iyalin su da kariyar dukiyoyin su, wallahi Malam Aminu sunfi wadnda ke dauke da bindiga na ta'addanci yawa.
 
Zuwa yaushe ka ke saran kammala binciken nan naka? Sannan bayan kammala binciken ka taya ka ke ganin zai amfani gwamnatoci wajen samar da tsaro?
 
To a hakikanin gaskiya inason in dan yi wata magana, naje wuce wa wata daba naga yara yan sha uku sha hudu sha biyar dauke da makamai masu tattalin kariyar kansu, gasu rike da makamai sai ka ga yaro da bindiga ya yi wata uku wata biyar be kashe ko kuje da'ita ba, na ke tambaya na ce toku ya rayuwarnan ta ke?, Suka ce ai su nan ba da dadewa ba barin wannan dabar za suyi, nicce kukoma wace?, su kace mu koma dabar wane,  sun fita aiki mu gamunan an barmu da dakon bindiga, mu ka yi sallah muka kare an gama addu'ar da za a yi cikin addu'a wani wanda ya bamu sallah ya ce jama'a ayi addu'a Allah ya kawo soja.
 
Cikin yan bindigan?
 
Cikin yan bindigan kuwa,  saboda mi? Saboda basu kashe kowa  da bindigan da ke gare su ta kariyar kai ce to a kan hakanan suke rokon Allah ya kawo soja saboda su gwada karfin bindiga wacce ke gare su , Allah be basu lamuni ba dako Allah ya kawo soja , yanayin da suke ciki Allah'n daya haliccemu da su suka sani suna da rai basu da rai Allah ya amshi addursu da ya kawo soja me yafari? sai kila in a kare wannan danbarwa sai mu gano abinda ake ciki.
Game da kai karshen bincike, kai karshen bincike nan Jami'a ta sawoni gaba na cewa ko inaso ko banso kona shirya ko ban shirya ba saina kare binciken nan karshen wannan shekarar, hakika littafi ne wanda na farashi shi shekara biyar da suka wuce na rubuta, kuma kullum dare da rana duk abinda ka gani ina kokarin inga na samu na kara, Allah ya kaddari an kama Emir na bungudu cikin dare jiya nittashi ni  ba da analysis cikin wannan littafin na sa bayanin inda ya kamata insa shi, abinda ya sa suke wadannan abun shine yau ko gobe za kaji suna maganar cewa gwamnatin idan tana son a sako wani abunda ta ce ana yi da yakin da ta ce anayi da halbe halben da kashe kashen da ake yi in anason su saki wani se anbari, to abinda na ke son a gane shine wannan aikin na kareshi aiki ne wanda ina da gehe sashe na daban na musamman wanda na aje a kan minene mahita? kuma mu tattauna da wadan nan yan bindiga sun fidda mahita.
 
Su da kansu?
 
Eh sun fidda mahita, misali abinda nake son ka sani, cikin wadannan mutanen da muke magana sai ka iske mutum da fiye da miliyan 20 cikin daji, miya gida nai babu magi babu gishiri babu nama babu mai, gashi da kudi amma babu lokacin minti guda najin dadi, duk inda ka ganshi to rataye ya ke da Bindiga, gashi yunwa da kishirwa da talauci ya ishe shi yana jan Bindiga Bindiga tana janai , amma kuma yana da dukiyar da baka yi tsammani ba, dukiyoyin na da ake magana ai sun samu kudi sun saye makamai ina tabbatar maka duk makamin da suke son su siye su Halilu su Shehu sun kawo masu, duk Bindigan da ka gani cikin wannan yankin mutanan nan ke kawota, basu bukatar kudin siyen makamai sun tara dukiya, naga wani wanda ya ce mun kuddi nai na cikin daji, gina rame ya yi ya turbude.
 
Menene kalamanka na karshe Dr Murtala Ahmad Rufa'i?
 
To kalamaina na karshe muna rokon Allah kuma zamu ci gaba da rokon Allah Ubangiji Allah ya gwada mana karshen wannan musibar lafiya.
 
To madalla muna godiya sosai.