Tinubu ya ayyana dokar-ta-ɓaci akan tsaro
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-baci kan tsaro a fadin Najeriya, tare da ba da umarnin daukar karin jami’ai a rundunonin tsaro domin shawo kan matsalolin tsaro da suka ta’azzara.
A wata sanarwa daga Fadar Shugaban Kasa, Tinubu ya ba da izinin daukar karin jami’an ’yansanda 20,000, wanda zai kai adadin da ake dauka zuwa 50,000, tare da amfani da sansanonin NYSC wajen horas da su. Ya kuma umarci a janye jami’an VIP guard domin horo na gaggawa kafin sake tura su yankunan da ke fama da tashin hankali.
Hukumar DSS ta samu umarnin tura dakarunta na daji da kuma daukar karin ma’aikata domin fatattakar ’yan ta’adda da ’yan bindiga da ke ɓoye a dazuka.
Shugaban kasar ya jinjinawa jami’an tsaro kan kubutar da dalibai 24 a Jihar Kebbi da mabiya addinin Kirista 38 a Kwara, yana mai tabbatar da ci gaba da kokarin ceto sauran wadanda ke hannun miyagu, ciki har da daliban da aka sace a Neja.
Tinubu ya bukaci Majalisar Dokoki ta Kasa ta fara duba dokar kafa ’yan sandan jihohi, tare da gargadin jihohi da su guji gina makarantu na kwana a wuraren da ba su da tsaro. Ya kuma bukaci masallatai da coci-coci su rika neman kariya daga ’yansanda.
Shugaban kasar ya mika ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasu a hare-hare a jihohin Kebbi, Borno, Zamfara, Neja, Yobe da Kwara, yana mai kira ga ’yan kasa su kasance masu kwarin gwiwa, su rika ba da hadin kai ga hukumomin tsaro.
managarciya