Mutane dubu 73 ne ke neman guraben aikin koyar wa dubu 10 a Kaduna

Mutane dubu 73 ne ke neman guraben aikin koyar wa dubu 10 a Kaduna

Akalla mutane dubu 73 ne ke neman guraben aikin koyar wa na makarantun firamare kusan 10,000 wanda hukumar kula da ilimin bai-daya ta jihar Kaduna, Kaduna SUBEB ta tallata.

Shugaban Hukumar SUBEB na Kaduna, Tijjani Abdullahi ne ya bayyana hakan a yau Litinin a Kaduna, lokacin da ake fara Jarrabawar daukar aikin ta na'ura mai ƙwaƙwalwa a cibiyar  Jami’ar Jihar Kaduna.

Abdullahi, wanda Mubarak Mohammed, wakilin dindindin na hukumar, ɓangaren ayyuka, ya wakilta, ya ce ana gudanar da jarrabawar a lokaci guda a cibiyoyi da ke a Kaduna, Zaria da Kafanchan.

Ya ce jarrabawar da za ta fara daga ranar 17 ga watan Oktoba zuwa 28 ga watan Oktoba, za ta yi tsauri sosai, inda ya ce za a dauki wadanda suka cancanta ne kawai.

“Zabar mutane 30,000 da za su zana jarabawar ta yanar gizo ita ce tangardar farko da aka yi ta. Rubuta jarrabawar ta na'ura mai ƙwaƙwalwa shine matsala ta biyu kuma wadanda suka samu nasara ne kawai za a tantance.

“Ina so in tabbatar wa jama’a cewa mafi cancanta ne kawai za a dauka aikin koyar da ƴaƴan mu.

"Wannan shine don gina ginshikin ilimi mai ƙarfi da ake buƙatar bunƙasa wa a cikin tafiyarsu ta ilimi," in ji shi.