Amfanin Kankana Wurin  Gyaran Fata Da Ba Ku Sani Ba

Amfanin Kankana Wurin  Gyaran Fata Da Ba Ku Sani Ba

Kankana na ɗaya daga cikin ‘ya’yan itace da ke da matuƙar tasiri a gyaran fata da kuma kawar da cututtukan fata masu dama. 

Tana ɗauke da sinadaran da ke gusar da maiƙon da ke fita a hanyoyin fitar gumi, wanda idan ya yawaita zai iya haifar da fesowar ƙananan ƙuraje.

Kankana na taka muhimmiyar rawa wajen gyara fatar da ta ke yawan yankwanewa, idan aka markaɗe ta (ba tare da an zuba mata ruwa ko kaɗan ba, kuma za a haɗe ne har ‘ya’anta) aka zuba mata zuma kaɗan, ana shafawa a inda matsalar ta ke sau biyu zuwa uku a rana.

A fuska tsayin mintuna 30 kafin a wanke da ruwan ɗumi don magance matsalar koɗewar fata, walau ta sanadiyyar zafin rana ko mutuwar ƙuraje, da sauransu.

Sai dai wannan haɗin ba shi da tasiri ga fatar da ta koɗe sanadin rashin abinda zai inganta ta na daga ɓangaren abinci ko ciyar da ita abinda ba ta buƙata na daga mayuka da kayan kwalliyar da ake amfani da su. Haɗin kan yi amfani ne bayan an kawar da matsalar, sai ya gyara ɓarnar da matsalar ta yi.

A ɓangaren rage bayyanar shekaru a fata, kankana na taimako ƙwarai idan aka tanadi man zaitun, nono kindirmo ( ba a amfani da nonon da yake da haɗi), ƙwai (kwaiduwar). Za a haɗe su tare da kankana ana shafawa duk dare a kwana da shi.

Ko kuma a samu ayaba a haɗa ta da kankanar da aka markaɗe sai a tarfa ruwa kaɗan a kwaɓa ana shafa wa fata.

Idan kuma gautsin fata ne matsalar ki ‘yar’uwa, za ki iya amfani da kankana don samun laushi a fatarki. 

Ta yaya? Ki daka ko ki markaɗe kankana, sannan ki haɗa ta da man riɗi, man kwakwa, sai man zaitun ( a kula, akwai fatar da ba ta cika son man zaitun ba, har tana sa ta yin baƙi.

Idan ta ki na ciki, sai ki zuba kaɗan ko ki cire shi daga kayan haɗin. Ya danganta da ƙiyayyar fatarki ga man). Ana shafa wannan haɗin da dare, tsayin minti talatin kafin a wanke.