Gidauniyar Ilimi ta ADDA Girl Education ta bai wa Dalibai 150 Tallafin Karatu a Gombe

Gidauniyar Ilimi ta ADDA Girl Education ta bai wa Dalibai 150 Tallafin Karatu a Gombe

 

Daga Habu Rabeel, Gombe

 

A kokarin ta na ci gaban harkar ilimi musamman na 'ya'ya Mata tsohuwar Alkalin kotun koli ta supreme court Mai Shari'a Zainab Adamu Bulkachuwa ta kafa Gidauniyar ilimin 'ya'ya Mata ta Adda Girl Education Foundation dake tallafawa wajen ci gaban  ilimi.

 
Gidauniyar a karon farko a watan Maris na wannan shekarar ta bai wa Yara 50 yan Makarantar Firamare da Sakandare da wasu dake Kwalejojin ilimi tallafin dan zurfafa karatun su a yankin karamar hukumar Nafada.
 
A ranar Talatar da ta gabata kuma a yankin karamar hukumar Akko ta sake zabo wasu Yara 50 'ya'yan marasa galihu ta sake basu tallafin karatun da ya hada da duk wani dawainiya na makaranta harda kudin Tara.
 
Hakazalika a wannan rana ta Laraba ta sake bai wa wasu 50 a kauyuka daban-daban a garin Talasse, dake karamar hukumar Balanga dan cika burin da ta dauka na tallafawa Yara 200 a fadin jihar.
 
Da take jawabi a wajen taron bada tallafin Mai sharia Zainab Bulkachuwa, ta yabawa Sarakunan gargajiya na yadda suke ba ta hadin kai da goyon baya wajen gudanar da wannan tallafi da take yi.
 
Bulkachuwa, wacce mai rikon Alkalin Alkalai ta jihar Gombe Mai sharia Halima S Muhammad ta wakilta tace shigowar sarakunan gargajiyar ya kara mata kwarin guiwar ci gaba da abunda take yi.
 
A cewar ta ta zabi bangaren Ilimin Mata ne dan ganin cewa 'ya'ya Mata musamman na kauyuka da basu da galihu sun sami ilimi kamar 'ya'yan kowanne mai galihu.
 
Ta kirayi masu hannu da shuni da su bada tasu gudumawar wajen ganin sun taimakawa Yaran inda a kalla kowanne mutum ya dauki dawainiyar akalla Yara 2 ko 3.
 
Da yake kaddamar da taron Sarkin Pindiga Ahmed Muhammad Seyoji, jinjinawa gidauniyar Adda Girl Education ya yi inda yace hakan kalubale ne ga Mazaje.
 
Basaraken ya yi kira ga dai dai ku da suyi koyi da Zainba Bulkachuwa wajen bunkasa harkar ilimi.
 
Ita ma manajar gudanarwa na gidauniyar Samira Galadima, cewa tayi gidauniyar Adda girl bayan bada tallafin karatu tana kuma samarwa da Yaran izinin shiga manyan makarantu na gaba da sakandare da kuma samar musu da aiki a gwamnati 
 
Samira, tace burin gidauniyar shi ne ta ga duk wata 'Ya Mace ta ilmantu domin Mata sune ginshikin al'umma.
 
Hadiza Mohammad da tayi magana a madadin daliban ta godewa Zainab Bulkachuwa kan wannan tallafi da ta yi musu