Sanatan Kaduna ya tsallake Rijiya da baya
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kaduna, Muhammad Rabiu, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan zargin yunkurin kashe Sanata Usman Lawal (PDP Kaduna-Central).
Umurnin binciken na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, Mansir Hassan, ya fitar ranar Alhamis a Kaduna.
Hassan ya ce, “’Yan sanda ba su san da yunkurin kashe Sanata Usman Lawal ba.
“An jawo hankalin hukumar ne ga wani buga a shafin Facebook na Sanata Lawal Usman.
Ya yi ikirarin cewa ya tsallake rijiya da baya a wani yunkurin kashe shi da wasu ‘yan daba suka yi a wani wurin da har yanzu ba a san ko su waye ba a Kaduna ta Arewa a ranar Laraba, kuma ba a bayar da lokacin faruwar lamarin ba.
Daga Abbakar Aleeyu Anache
managarciya