Kona Qur'an A Sweden: Ba Za Mu Lamunta Ba---Sarkin Musulmi

Kona Qur'an A Sweden: Ba Za Mu Lamunta Ba---Sarkin Musulmi

 

Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar ya yi Allah wadai da kona Alkur’ani a bakin masallacin birnin Stockholm na kasar Sweden. 

Ya bayyana wannan aika-aika a matsayin cin zarafi da kuma neman tsokana wanda ya sabawa dokokin kasashe.
Sultan ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da mataimakin sakatare janar na Majalisar Kula da Harkokin Addinin Musulunci (NSCIA), Farfesa Salisu Shehu ya fitar a ranar Asabar 8 ga watan Yuli. 
Ya ce yadda kasashen Turai ke tozarta duk wasu abubuwa da suka shafi Musulunci ya nuna a fili rashin adalcinsu, cewar Premium Times. 
Ya bukaci Musulmai da su kai zuciya nesa inda ya kiraye gwamnatin Sweden da su yi binciken gaggawa tare da daukar mataki.
 “Abin mamaki ne irin wannan sabo mai girma ta faru a kasar da ake ganin na daga cikin kasashe masu son zaman lafiya a Nahiyar Turai. 
“Wannar majalisar ta kadu da jin haka a kasar inda ‘yan sandan su da ke ikirarin wayewa da sanin aiki suka gagara daukar wani mataki, inda suka ba da dama ga wani don aikata wannan kwamacala."