Majalisar Dokokin Adamawa Ta Amince A Rika Yin Gwajin Shaye-Shaye Ga Dalibbai Da Masu Neman Aiki A Jihar

Majalisar Dokokin Adamawa Ta Amince A Rika Yin Gwajin Shaye-Shaye Ga Dalibbai Da Masu Neman Aiki A Jihar

 

Daga  Ukasha Ibrahim

 

Majalisar dokokin jihar Adamawa ta amince da kudirin gwajin yin shaye-shaye yayin neman aiki ko kuma neman shiga makarantar gaba da Sikandare a kaf fadin jihar.

 
Kudirin wanda dan majalisa mai wakiltar Yola ta kudu, Honarabul Kabiru Mijinyawa  ya gabatar gaban majalisar wanda  zai tilastawa masu neman aiki da masu bukatar shiga manyan makarantu a jihar ta Adamawa yin gwajin shan giya ko shan  miyagun kwayoyi kafin daukar su aiki ko kuma shiga manyan makarantu, 
 
Kudirin dai ya samu marawar mataimakin shugaban masu rinjaye na majalisar mai wakiltar Gombi  Hon. Japhet Kefas 
 
Bayan aminta da kudirin, kakakin majalisar dokokin jihar Adamawa, Rt. Hon. Iya Abbas ya bada umarnin fara yin shiri domin mikawa gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri wanan kudirin domin sa hannu, kamar yadda shashin Yola 24 English ta ruwaito.