Babban Hafsan Tsaron Najeriya Ya Gana  Da Gwamnan Zamfara a Abuja

Babban Hafsan Tsaron Najeriya Ya Gana  Da Gwamnan Zamfara a Abuja
 
Babban hafsan tsaron ƙasa (CDS), Manjo Janar Christopher Musa na gana wa yanzu haka da gwamnan Zamfara, Dauda Lawal a hedkwatar tsaro da ke Abuja.
Duk da ba bu cikakken bayani dangane da maƙasudin wannan zama har zuwa yanzu da muka haɗa muku rahoto, ana ganin taron zai maida hankali kacokan kan kalubalen tsaron da ya addabi Zamfara.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa gwamna Lawal ya isa babbar hedkwatar tsaron rundunar soji da misalin ƙarfe 12:22 na rana yau Laraba tare da rakiyar wasu hadimansa. 
Haka zalika an ga lokacin da babban hafsan tsaro na ƙasa tare da manyan jami'an soji suka shiga ɗakin taro da gwamnan, kamar yadda rahotanni suka tabbatar. 
Wani jami'i, wanda baya son a ambaci sunansa, ya shaida wa jaridar cewa a yanzu an zura wa rundunar sojin Najeriya ido domin ganin yadda zata magance lamarin 'yan bindiga a Zamfara. 
A cewarsa, wannan ne babban batun da ya sa babban hafsan tsaro da gwamna Lawal suka sa labule yau Laraba, 12 ga watan Yuli, a birnin tarayya Abuja. 
"Bayan taya juna murna, zasu tattauna da lalubo dabarun magance matsalar tsaron da ta addabi jihar gwamna Lawal da sauran jihohin ƙasar nan," inji shi. 

managarciya.com