Ganduje ba shi da ikon kafa Hisbah a Kano — Lauya Dantani
Lauya kuma mai fafutukar kare haƙƙin ɗan Adam, Hamza N. Dantani, ya soki shirin tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, na kafa wata Hisbah mai zaman kanta domin jami’ai 12,000 da aka sallama.
A wata sanarwa da ya fitar, Dantani ya ce wannan mataki ya sabawa Kundin Tsarin Mulki na 1999, yana kuma iya haifar da tashin hankali a jihar.
Ya ce Ganduje ba shi da ikon gudanarwa a matsayin tsohon gwamna, sannan doka ta tanadi cewa gwamna mai ci shi ne shugaban gudanarwar jiha.
Dantani ya bayyana cewa Kano na da hukumar Hisbah bisa doka, kuma gwamna da majalisar dokoki ne kaɗai ke da ikon gyarawa ko sake tsara ta.
Ya kuma yi gargadin cewa tsarin da Ganduje ke shirin kafa wa ya yi kama da ƙungiyar ‘yan banga, abin da Kundin Tsarin Mulki ya haramta.
A cewarsa, kafa wata Hisbah a waje da ikon gwamnati ba bisa doka ba ne, kuma ka iya zama dabara ta siyasa da nufin kalubalantar gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Lauyan ya bukaci Ganduje da ya janye shirin domin kauce wa rikici da tabbatar da mutunta tsarin mulki.
managarciya