'Yan Bindiga Sun Sake Sakin Mutane 5 Da Suka Yi Garkuwa Da Su A cikin Jirgin Kasa Daga Abuja Zuwa Kaduna
Daga Jabir Ridwan Sokoto.
Rahotanni sun bayyana cewa a ranar talata ne Yan bindigar nan da sukayi garkuwa da mutane da dama a cikin harin da suka kaiwa Jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna Sun saki wasu mutun biyar.
Idan dai za'a iya tunawa 28 ga Watan maris ne Yan bindiga suka kai wa Jirgin kasa da yataso daga Abuja zuwa Kaduna hari inda sukayi garkuwa da mutane da dama.
Hakama makonnin da suka gabata ne Yan bindiga suka fitar da wani faifan bidiyo Mai Nuna yadda suke azabtar da mutane da sukayi garkuwa dasu, inda mutanen ke kira da hukumomin kasashen duniya da sukawo musu dauki.
Daga cikin wadanda Yan bindigar suka Sako akwai wani Mai suna Mukhtar Shu'aibu Wanda yqj bindigar suka harba sakamakon musayar wuta a yayin harin Amma sai dai Bai mutu ba.
Mai shiga tsakani da Kuma sulhu da Yan bindigar da Kuma gwamnatin tarayya tukur Mamu Wanda a Baya ya janye kanshi daga sulhu yakuma sake dawowa shine ya tabbatarda sakin mutanen a jahar Kaduna.
managarciya