PAN Ta Shirya Taron Wayar da Kan Mambobinta Yadda Ake Kiwon Kaji A Zamance

PAN Ta Shirya Taron Wayar da Kan Mambobinta Yadda Ake Kiwon Kaji A Zamance
PAN Ta Shirya Taron Wayar da Kan Mambobinta Yadda Ake Kiwon Kaji A Zamance

Kungiyar manoman kaji a jihar Neha ( Poultry Association Of Nigeria) ta shiryawa horon wayar da kai yadda ake kiwon kaji. Da yake bayani a lokacin bude taron na yini daya, shugaban kungiyar, Hon. Muhammad Usman Saba, yace mun shirya wannan taron ne dan tattaunawa akan matsalolin da muke fuskanta akan kiwon kaji da kuma lalubo hanyoyin da mambobin mu zasu gajiyar tallafin bankin CBN da take baiwa manoma.

Yace yanzu haka PAN tayi hadin guiwa da wasu manyan kamfanoni da yan kasuwa ta yadda za mu rika samun kayan aiki a saukake da kuma yadda za mu daga darajar kasuwancin kaji da kwan kaji dama duk wani abu mai muhimmanci da kaji ke samarwa dan mu samu damar cin anfanin abinda muka dogara da shi na kiwon kaji.
Yace yanzu haka mun samu daidaito da bankin CBN ta hannun bankin Sterling ta yadda mambobin mu zasu ci gajiyar tallafin manoma, wanda kuma mun yi nisa da shirye shirye da bankin NIRSEL dan ganin mun ci gajiyar tallafin ta na bangaren noma.
Hon. Saba, yace muna yunkurin samar da kasuwan kaji a garin minna, wanda ya ba mu damar cigaba da horar da tsoffin mambobin mu da ma wadanda ke shirin shigowa, don horar da masu kiwon kaji sanin dubarun kiwon da kuma irin matakan da ya kamata su dauka wajen kare kajin su daga annobar da kan shafi kajin.
Yace yanzu haka bisa kididdiga jihar nan kan gaba da sauran jahohi wajen noman kaji, yace kan haka CBN ta sha alwashin tallafawa manoman kaji da ke karkashin kungiyar PAN da naira miliyan uku ko wannan su tare da samar da kwararru a bangaren kiwon kaji da zasu taimaka masu da shawarwari dan bunkasa noman kaji da kasuwancin sa a jihar.
Da yake jawabi, kwamishinan ma'aikatar dabbobi, Malam Haruna Dukku, yace yawan kaji da kwan da ake anfani da su shigo da su ake yi daga makotan jahohi, alhalin jihar na da karfi da yanayin da zasu iya samar da kaji da sauran dabbobin da ake kiwo har wasu jahohin su anfana, fiye da wadanda ake kawo mana.

Dan haka ina jawo hankalin masu kiwon kaji musamman yayan kungiyar PAN da cewar ma'aikatar mu a shirye take wajen hada kai da bankuna dan samar maku da tallafi saboda mu karfafa guiwar ku.
Kungiyar dai ta samu tallafin ton xari da ashirin na masara akan naira dubu goma sha takwas, wanda ita kuma saboda wahalhalun da aka yi wajen karbo masarar za ta baiwa manoman akan naira dubu goma sha takwas da dari tara, jimlar kudin masarar da aka samar dan yin abincin kajin ya kai adadin kudi naira miliyan ashirin da daya a cewarsa.
Taron dai ya samu halartar kwararru daga ma'aikatar kiwon dabbi bisa jagorancin kwamishina Malam Haruna Dukku da babban sakataren ma'aikatar  Dokta Jonathan Wasa, sai wakilan bankin CBN da Sterling da kuma bankin inshora na NAIC.