Magidanci Ya Nemi Alkali Ya Raba Aurensa Da Matarsa Domin Bata Sallah Kuma Ta Tsani Mahaifiyarsa

Magidanci Ya Nemi Alkali Ya Raba Aurensa Da Matarsa Domin Bata Sallah Kuma Ta Tsani Mahaifiyarsa

 

Wata kotu mai matsayi na farko dake yankin Kubwa ta babban birnin tarayya ta kashe aure mai shekaru 19 tsakanin dan kasuwa Lukman Abduaziz da matarsa Rashidat kan banbance-bancen da aka gaza shawo kansu. 

Alkalin mai suna Muhammad Adamu, ya tsinke auren saboda Abdulaziz ya roki tabbatar da sakinsa kamar yadda addinin Islama ya tanadar. 
Magidanci ya bayyana sakin matarsa da yayi saboda tsabar tsanar mahaifiyarsa da tayi kuma bata sallolinta 5 na rana Kamar yadda Lukman Abdulaziz ya sanar, ya kauracewa matarsa Rashida kuma a yanzu ta kammala iddarta Rashidat ta sanar da cewa ba za ta bar gidan shi ba saboda tare suka gina a matsayin mallakin yara hudun da suka haifa. 
Daily Nigerian ta ruwaito cewa, Adamu wanda yace a Musulunci mutum yana da damar sakin matarsa yace Rashidat ta sanar da kotu cewa ta kammala iddarta. 
Yace Rashidat ba matarsa bace kuma an shawarce sa da su je su samu lokaci tare da tattaunawa kan yadda za su tarbiyyantar da yaransu hudu. 
Alkalin yace kotu zata bada shaidar rabuwar auren. Tun farko, Abdulaziz ya sanar da kotun cewa ya kasa shawo kan matsalar dake tsakaninsa da matsar kuma ya sake ta amma yana neman tabbaci daga kotu. 
“Ba ta yi sallolinta na kowacce rana kuma bata kaunar 'yan uwana. 
Na bukaci ta bi ni kauye yadda zamu sasanta kan dalilin da yasa bata kaunar mahaifiyata amma ta ki.
 
"Na saketa a ranar 6 ga watan Yuni kuma ta kammala iddah. A yanzu bani da ra'ayin rayuwar aure da ita kuma na sanar da iyayenta,". 
A martanin Rashidat, ta sanar da kotun cewa Abdulaziz ya sanar da ita a ranar 27 ga watan Augusta, baya kwanciyar aure da ita na watanni uku da suka wuce saboda yana son sakinta. 
"Yace zai kula da yaranmu hudu amma yana son in bar masa gidansa saboda zai siyar da shi. 
"Na sanar masa cewa gidan mallakin yarana ne saboda tare muka gina, ba gidansa ba ne,"