Ƙungiyar lauyoyi ta Najeriya ta nemi a dakatar da aiwatar da sabbin dokokin haraji
Kungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA) ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta dakatar da aiwatar da Dokokin Gyaran Haraji sakamakon cece-kucen da suka taso kan yadda aka samar da su.
Shugaban NBA, Mazi Afam Osigwe, SAN, ya ce rigingimun da ke tattare da dokokin sun jefa shakku kan gaskiya, sahihanci da amincin tsarin dokoki na kasa.
Ya bayyana haka ne biyo bayan zargin da wani dan Majalisar Wakilai, Hon. Abdulsammad Dasuki, ya yi na cewa akwai sabani tsakanin dokokin majalisar tarayya ta amince da su da kuma sigar da aka wallafa ga jama’a.
NBA ta ce wajibi ne a gudanar da cikakken bincike a fili domin fayyace gaskiyar lamarin tare da dawo da amincewar jama’a ga tsarin majalisa.
Kungiyar ta jaddada cewa aiwatar da dokokin ya kamata a dakatar da shi har sai an warware dukkan matsalolin da ke tattare da su.
A cewar NBA, rashin tabbas a bangaren doka da manufofi na iya illata yanayin kasuwanci, rage amincewar masu zuba jari, tare da barazana ga daidaiton tattalin arziki da bin doka da oda a Nijeriya.
managarciya