Kungiyar Kwadago Ta Ce Babu Ja Da Baya a Yajin Aikin Da Take Shirin Shiga

Kungiyar Kwadago Ta Ce Babu Ja Da Baya a Yajin Aikin Da Take Shirin Shiga

Kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta bukaci daukacin al'ummar Najeriya da su shiga cikin "gangamin neman yanci", inda ta dage cewa za ta shiga yajin aikin sai baba ta gani daga ranar Talata.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar NLC, Joe Ajaero, ya fitar a safiyar ranar Lahadi, 1 Oktoba, na bikin cikar kasar shekaru 63 da samun ‘yancin kai. 
 
Ya sanar da yan Najeriya cewa za su cimma nasara idan suka tsaya tsayin daka a matsayin kungiya da ba za a iya raba kanta ba, Channels TV ta rahoto.
Ajaero ya bukaci dukkan masu masu fada aji a kasar, musamman masu rike da sarautun gargajiya da su roki gwamnati ta sauke nauyin da ke kan jama’a, rahoton The Guardian. 
A tare, za mu iya dawo da darajar da ya kubce mana tsawon lokaci. Lokaci ya yi da Najeriya za ta tashi ta sake haskawa a matsayin fitilar fata da wadata ga daukacin al'ummarta.
"Ku tuna, idan muka tsaya a matsayin tsintsiya madaurinki daya muka hana a raba mu, za mu yi nasara! Muna kira ga daukacin yan Najeriya da su kasance tare da mu a ranar 3 ga watan Oktoba a fadin Najeriya domin fara tattakinmu na neman yanci ta hanyar yajin aikin gama gari har sai baba ta gani."