'Yan Bindiga Sun Sace Mutum 11 Ciki Har Da Tsohuwa Mai Shekara 70 A Jihar Taraba

'Yan Bindiga Sun Sace Mutum 11 Ciki Har Da Tsohuwa Mai Shekara 70 A Jihar Taraba

'

'Yan bindiga sun sace mutum 11 a kauyen Illela dake cikin karamar hukumar Karim-Lamido a Jihar Taraba dake arewacin Nijeriya.

Wata majiya ta shaidawa manema labarai maharan sun shhiga kauyen da tsakar daern ranar Alhamis data gabata in da suka tafi da mutum 11 ciki har da tsohuwa mai shekara 70. 

Tsohuwar ta rasa ranta a wurin masu Garkuwan kamar yadda wasu mutum biyu da suka kubuta suka sanar.
Dagacin garin Zip Alhaji Uba ya shaidawa wakilin Aminiya cewa Dan sa Mai suna Buhari na daga cikin mutanen da aka sace Kuma har har yanzu yana hannun wadanda suke sace su. 
Ya bayyana cewa masu sace mutanen sun bukaci a biya su kudi Naira miliyan Saba'in a matsayin kudin fansa.
Kakakin rundunan  'yan sanda na Jihar Taraba,DSP Usman Abdullahi ya tabbatar da aukuwar wanna lamarin.