Dukkan Gwamnonin Nijeriya sun damu da rikicin da ke faruwa a jihar Filato-----Tambuwal

Dukkan Gwamnonin Nijeriya sun damu da rikicin da ke faruwa a jihar Filato-----Tambuwal
Dukkan Gwamnonin Nijeriya sun damu da rikicin da ke faruwa a jihar Filato-----Tambuwal
 
Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana cewa dukkan gwamnonin Nijeriya sun damu da wannan rikicin da yake faruwa a jihar Filato.
Ya tuna cewa a watan Maris na 2017 gaba daya majalisar zartarwarsa tare da Sarkin musulmi suka zo Jos yin taron sanin makamar aiki, "Mun yi haka ne a wancan lokacin don mu nuna wa duniya zaman lafiya ya dawo a jihar Filato, mu kara nuna duniya mutanen Sakkwato kamar sauran 'yan Nijeriya sun dauki jihar Filato gida ce."
"Dole mu zauna tare da juna a matsayin 'yan uwa domin ba addini da ya aminta kashe juna, don mi za mu rika labewa da sunan addini ko kabilanci muna kisan junanmu?" a cewarsa.
"Mu zauna lafiya da junanmu, ba wani mutum da zai zo ya zuba jari matukar ba mu da kwanciyar hankali, zaman lafiya nauyi ne da ya rataya saman kowa, jami'an tsaro ba su iya komai in ba mu hada kai muka yi aiki tare ba."
Ya yi kira ga mutanen Nijeriya su bi koyarwa addini yanda ta tanadar.
Tambuwal a wurin taron masu ruwa da tsaki da aka yi a Jos ya ce tashin hankali hasara kawai yake haifarwa yakamata mutane su rungumi zaman lafiya.