Gwamnan Sokoto Ya Fadawa Jami'an Tsaro Matsayin Rundunar Tsaron Al'umma Da Ya Kafa 

Gwamnan Sokoto Ya Fadawa Jami'an Tsaro Matsayin Rundunar Tsaron Al'umma Da Ya Kafa 

 

A ranar Alhamis ne gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya sanya hannu a kan kudirin dokar samar da jami'an tsaron al'ummar Sokoto. 

A ranar 21 ga watan Disamba ne majalisar dokokin jihar ta amince da kudirin gwamnan na kafa jami’an sintiri a jihar. 
Da yake rattaba hannu kan kudirin dokar a gidan gwamnati, Gwamna Aliyu ya ce gwamnatinsa ta kafa rundunar tsaron don tallafawa kokarin gwamnatin Bola Tinubu na samar da isasshen tsaro ga al’umma. 
Ya kara da cewa jami'an tsaron al'ummar ba kishiyar ‘yan sanda ba ne.
"Rattaba hannu kan wannan doka ta samar da jami'an tsaron Jihar Sokoto wani muhimmin cigaba ne a rayuwar wannan gwamnati da jama'a baki daya. 
“Kamar yadda muka sani, jihar Sokoto na fuskantar matsalar rashin tsaro, musamman ‘yan fashi da makami, wanda hakan ke kawo ruguza yanayin zaman lafiya da aka san jihar da shi." 
"Kirkirar wannan jami’an tsaro an yi shi ne domin kara yunkurin samar da tsaro na yau da kullun don kare rayuka da dukiyoyin al’umma. 
“Bari in fada a fili cewa jami’an tsaron al’umma ba kishiyar ‘yan sandan Sokoto ba ne, gwamnatin jihar ba ta kirkiro jami'an tsaron don zama kishiyar 'yan sanda ba.” 
Ya yi kira ga jami'an tsaro a jiha da su ba da goyon baya ga jami'an don cimma burin da ake da shi na samar da tsaro a jiha da kasa baki daya.