Gwamna Zulum Ya Taya Sabbin Shugabannin NUJ Jihar Borno Murna

Gwamna Zulum Ya Taya Sabbin Shugabannin NUJ Jihar Borno Murna

Daga Muhammad Maitela, Maiduguri.

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya taya sabbin zababbun shugabannin kungiyar yan jaridu ta Najeriya (NUJ) murna, bisa zaben sabbin shugabannin da kungiyar ta gudanar ranar Asabar, a Sakatariyar Musa Usman da ke birnin Maiduguri a jihar Borno.

Sakon taya murnar da Gwamna Zulum ya na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labaru mai dauke da sa hannun mai magana da yawunsa, Malam Isa Gusau wadda ya fitar ranar Lahadi.

Bugu da kari, a kebance Gwamnan ya mika sakon taya murna ga sabon shugaban kungiyar ta NUJ a jihar Borno, Kwamared Dauda Iliya, na gidan Rediyon Tarayyar Najeriya (FRCN).

Haka kuma Zulum ya taya AbdulKareem Haruna, mawallafin jaridar 'Humanitarian Times' murna wanda aka zaba a matsayin mataimakin shugaban Kungiyar, da Ali Chiroma na Peace FM dake Maiduguri, wanda aka zaba a matsayin sakatare.

Sannan kuma Gwamnan ya yaba wa shugaban kungiyar NUJ a jihar Borno; mai barin gado, Kwamared Babagana Bukar bisa yadda ya nuna bajinta wajen amincewa da shan kaye a zaben kana da yadda ya jagoranci Kungiyar wajen gudanar da sahihin zabe.

Har wala yau, ya taya sauran shugabannin, wadanda suka hada da Hauwa Bata ta Peace FM- a matsayin ma'aji, Iya Ma'aji NTA- Mataimakin Sakatare, Babagana Ali na BRTV (Gidan Rediyo da Talabijin jihar Borno)- Sakataren Kudi da Babagana Liman na Ma’aikatar Watsa Labarai ta Jihar Borno- a matsayin mai binciken kudi.

Gwamna Zulum ya yaba wa yan jaridun da suke aiki a jihar Borno bisa irin kyakkyawan alaka tare da gudanar da ayyukan su cikin tsanaki, musamman irin yadda suka gudanar da wannan zabe cikin lumana, al’amurin da ya kamata a koya daga kungiyar NUJ. Kana ya yaba wa jami’an shalkwatar NUJ ta shiyyar arewa maso gabas da suka sanya ido wajen ganin zaben ya yi armashi.

Gwamnan ya umurci mataimakan sa kan harkokin yada labarai da su bai wa sabbin shugabannin cikakken goyon baya, musamman ci gaba da kyakkyawar alaka kuma mai dorewa da yan jarida tare da gudanar da ayyukansu cikin yanci, samun tabbacin basu bayanai, kula da jin -dadin yan jaridu da daukar nauyin horar dasu, idan sun nemi goyon bayan gwamnati.

Sanarwar ta kara da cewa, a kokarin Kungiyar na gudanar da zaben, Gwamna Zulum ya taka muhimmiyar rawar ta hanyar tallafa wa NUJ da kudade domin gudanar da wannan zaben cikin lumana da kuma kin amincewa da tsoma baki a harkokin zaben, wanda ya kai ga sakarwa mambobin Kungiyar su yi uwa da makarbiya wajen zaben shugabanin da suka dace.

A halin da ake ciki yanzu, Gwamna Zulum, ya umurci masu taimaka masa kan harkokin yada labarai da su tabbatar da gudanar da wani horo kan yadda za a gudanar da zabuka, tare da tabbacin halartar yan jaridu 100 a karkashin kungiyar NUJ ta Borno, da hadin gwiwa sashin yada labarai na fadar gwamnati dake Maiduguri da tsangayar Koyar da Ilimin Aikin Jarida (Department of Mass Communication) na Jami'ar Maiduguri.