Ina Aka Kwana Kan Alkawalin Tambuwal Na Bayar Da Fili A Gina Jami'ar Mata Da Sarkin Musulmi Ya Kudiri Kafawa Sama Da Shekara 10 Da Suka Wuce
Tabuwal ya ce tun kafin Turawan mulkin mallaka su zo kasar nan daular Usmaniya tana da tsarin shugabancinta da ya daure har yanzu. Da farko Sarkin Kabin Argungu Alhaji Sama'ila Muhammad Mera kuma shi ne jagoran gidauniyar Sarkin Musulmi ya godewa gwamna amadadin Sarkin Musulmi yanda ya hana masu yin bara domin samun kudin buga littafan. "Mun tattara littafan mujaddadi da kanensa da dansa, mun gano akwai wadanda ba jingina masu ne kawai aka yi da wadanda aka sanya abin da ba su suka ce ba, da farko mun buga littafai 98 aka fassara da Larabci da Hausa da Turanci, aikin ya kwashe shekara biyar muna yinsa." Ya ce aikin ya lakume miliyan 20 sun buga littafai miliyan daya da dubu shidda da hamsin.
Domin ganin an tabbatar da gina jami’ar mata zalla da za ta fi bayar da karfi ga karatun likitanci a jihar Sakkwato.
Gwamnan jihar Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya ba da sanarwar gwamnatinsa za ta samar da fili domin fara gina jami’ar, ba da bata wani lokaci ba.
Jami’ar Nana Asma’u ta karatun likitanci ce ta Mata da gidauniyar Sarkin Musulmi ta kirkira take son ta gina shekara fiye da shekarru 10 da suka gabata.
Gwamnan ya yi maganar ne a lokacin da yake karbar littafan malaman daular Usmaniya da gwamnatinsa ta dauki nauyin a buga su sama da shekara daya da ya wuce.
Ya umarci ma’aikatar filaye da gidaje ta samar da kyakkyawan fili domin soma aikin. Ya ce gwamnatinsa a shirye take ta bunkasa aiyukkan shugabani na yanzu da wadan da suka gabata na daular Usmaniya.
Tabuwal ya ce tun kafin Turawan mulkin mallaka su zo kasar nan daular Usmaniya tana da tsarin shugabancinta da ya daure har yanzu.
Da farko Sarkin Kabin Argungu Alhaji Sama'ila Muhammad Mera kuma shi ne jagoran gidauniyar Sarkin Musulmi ya godewa gwamna amadadin Sarkin Musulmi yanda ya hana masu yin bara domin samun kudin buga littafan.
"Mun tattara littafan mujaddadi da kanensa da dansa, mun gano akwai wadanda ba jingina masu ne kawai aka yi da wadanda aka sanya abin da ba su suka ce ba, da farko mun buga littafai 98 aka fassara da Larabci da Hausa da Turanci, aikin ya kwashe shekara biyar muna yinsa."
Ya ce aikin ya lakume miliyan 20 sun buga littafai miliyan daya da dubu shidda da hamsin.
"A kashi na biyun nan Tambuwal ya ce ba sai mun yi yawon bara ba ya ba mu miliyan 98 kashi hamsin na fara aikin ga shi aikin ya kammala duk da wasu jarabawowi da aka samu. An buga littafan miliyan daya da dubu 300 da 80". A cewarsa.
Ya ce littafai ne da suka yi magana kan tsaro da shugabanci da sauran mu'amala.
Domin sanin in da aka kwana kan wannan alkawalin da gwamnati ta yi wakilinmu ya tuntubi kwamishinan ma'aikatar filaye da gidaje ta jiha Honarabul Aminu Bala Bodinga amma bai dauki wayarsa ba.
managarciya