Kitso sana'a ce da ta dace da kowane zamani

Kitso sana'a ce da ta dace da kowane zamani

                                                                      KITSO

   Tun kan a haifi uwar mai sabulu Balbela take da farin gashin ta. Kitso na daya daga cikin abin yin kawa ga mata a cikin kowace al’umma a duniyar nan. Masana tarihi sun yi iya kokarin gano yaushe ne yin kitso ga mata ya zama al’ada abin ya ci tura, babban abin da aka yi ittifaki akai shi ne, kitso na cikin al’amurran kawa da bil’Adama ya dauka tun farkon samuwar sa a bayan kasa.

   Kamar sauran al’ummomin duniya, matan Hausawa na yin kitso kuma su na ba shi muhimmancin da ya kamata. Domin yin kitso ko gyaran gashi na daga cikin alfarin ‘ya mace a tsakanin tsaranta, wata kila shi ne dalilin da yasa Bahaushe yayi amfani da wannan wajen yin karin maganar sa da yake cewa “In ba ki da gashin wance ba ki kitson wance”.

    A kasar Hausa ma kitso ya zama sana’a ga wasu mata dake yiwa sauran ‘yan uwan su mata kitson a duk lokacin da bukatar haka ta taso. Mai wannan sana’ar ita ake kira MAKITSIYA  ko Mai Kitso.

    Domin samun karin haske Mujallar Managarciya  ta samu tattaunawa da wata mai wannan sana’ar kuma kwararra a fanni kitso wacce ke zaune a anguwar Gawon Dannunu, Tudun Wada da ke nan cikin garin Sakkwato mai suna Maimuna Abubakar, in da muka samu bayanai kamar haka;

  Kashe-kashen kitso a kasar Hausa: Akwai kashe-kashen kitso da dama da muka sami kakanni  da uwayen mu na yi, can da ba wasu nau’in kitso ke akwai da yawa ba, kawai mace ta yi kitso, amma daga baya an samu wasu nau’o’in kitso kamar Zanen Yawo, Kwandon kifi, Tukkuwa, Shaku,  tsoro shidda da mai ayaba. Daga baya kuma an samu karin wasu da suka hada da mai ayaba, Kabarin Murtala, gadar Jebba  da juyin mulki.

   Chudanyar mu da wasu al’ummomi da  kabilu a wannan zamani ya sa wasu nau’o’in kitso sun shigo a kasar Hausa da suka hada da Igberra style (watau kitson kabilar Iberra da ke jihar Kogi) Ghana weaving, two babies, kiss me, da police cap.

   Kitso zai zama ko dai kitse ko weaving ya danganta daga wurin daukar, watau yadda za’a saka kitson ko dai ya zama gaba-gaba ko a fara shi daga baya.

   Abubuwan da ake bukata  domin yin kitso: A kowane lokaci dole ne shi tsinke ya kasance akwai shi, wanda ya ke kamar matsayin aska ga wanzami, ba yadda za’a yi kitso ba tare da tsinke ba, dole kuma ya zama mai tsini sosai sai dai a madaukin sa (holder) ya kan banbanta  daga wannan zuwa wancan. Sai kuma mashacin kai ko matsefi (comb) ke nan, wadannan su ne manya. Sai kuma man shafi, can da kakannin mu su na amfani da ko dai man kade ko man shanu, wanda ‘yan matan yanzu ke ganin su na sa wari a kai, sai dai kin san yanzu an fara inganta man kade domin ya tafi daidai da zamani ana kiran sa (sheabutter).

  A yanzu akwai kalolin man kitso har ba su kirguwa, ya danganta daga abin da mace ta ke so, akwai na gyaran gashi da tsawon gashi da masu maganin amosanin kai da na laushin gashi. Wadannan kalolin man kitson sun hada da Kuza, coconut oil, pick oil, sheabutter (man ka]e) formula 10 da kuma Dark. Akwai wasu kuma daban.

A yini mace nawa ake iya yiwa kitso: ya danganta daga wane iri kitso za’a yi ko ya yawan gashin wacce za’a yiwa kitson. Misali idan amarya ce, dole kitson zai dau lokaci domin dole a fito da ita sosai.

   Matsaloli: ba za a rasa ‘yan matsaloli a harakar kitso ba, kamar yadda na fada a sama ya na da kyau, a jiye sirrin kowa daban. Duk wacce ki ka rika kanta sai ta zo maki da na ta magana ko dai don neman shawara ko don gulmar abokiyar zaman ta ko wata fira ta daban. Yana da wuya ba’a samu wannan ba. Abu na biyu, kasancewar halin da muke ciki a yanzu na bazuwar cuta a cikin al’umma, mafi yawan masu zuwa kitso sun fi son zuwa da tsinke da matajen(comb) kan su, domin kiyayewa da amfani da na wani (Allah Ya karemu).

   Gwamnati  ba ta cika daukar sana’ar kitso a matsayin sana’ar da za’a sanya a cikin jerin kananan sana’o’in hannu ba, wannan na daga ciki matsalolin da sana’ar kitso ke fuskanta a halin yanzu.

   Nasarori: akwai samun  kudin shiga,  babbar nasarar wannan sana’a ba kamar zumunta, kin san mu mata muna da saurin kulla zumunta. Akwai mutane da yawa da wannan sana’a ta sanya sun zama kawaye  da ‘yan uwan taka ta kud da kud.