Bayan Shan Suka, daga Karshe an Dage Taron 'Qur'anic Convention' da Aka Shirya a Abuja 

Bayan Shan Suka, daga Karshe an Dage Taron 'Qur'anic Convention' da Aka Shirya a Abuja 

 
Rahotanni sun tabbatar cewa an ɗage taron 'Qur'anic Convention' da aka shirya yi a Abuja a karshen watan Fabrairun 2025. 
An dage taron ne wanda ake sa ran zai haɗa mahaddata Qur'ani sama da 60, 000 daga ciki da wajen Najeriya. 
Rahoton BBC Hausa ya ce an saka ranar Asabar 22 ga watan Fabrairu, 2025 a matsayin ranar da za a gudanar da taron. Wannan na zuwa ne kwanaki ƙadan bayan shugaban Izalah, Sheikh Bala Lau ya ce a shirye suke su karbi gyara kan shirin 'Qur'anic Convention'. 
Yayin jawabinsa, Sheikh Bala Lau ya bukaci sauran kungiyoyin Izalah da al'ummar Musulmi su mara wa shirin baya. 
An yi fatan taron zai jawo hankalin mahaddata Alkur'ani da dama, amma yanzu an ɗage shi ba tare da bayyana sabuwar ranar ba. 
Wani ɗan kwamitin shirya taron wanda bai so a ambaci sunansa ba ya tabbatar cewa: "Tun daren  Alhamis 13 ga watan Janairun 2025 aka ɗage yin wannan taro." 
Sai dai  jami'in da ke cikin kwamitin bai bayyana dalilin ɗagewar ko lokacin da za a sake yin taron ba. 
Amma kuma majiyar ta tabbatar da cewa ana sa ran bayan watan Ramadan za a iya sanya rana domin gudanar da taron. 
Taron ya sha suka a cikin mutanen Arewa in da mafi yawan jama'a suka tafi kan taron nada alaka da siyasa.
Da yawan mutane sun zargi gwamnatin Nijeriya ce za ta dauki nauyin taron domin ganin ta cika burinta na sake samun nasara a 2027.