An Shiga Jimamin Bacewar Yarinya Bayan Kwale Kwale Ya Kife da Yan Kasuwa a Jigawa 

An Shiga Jimamin Bacewar Yarinya Bayan Kwale Kwale Ya Kife da Yan Kasuwa a Jigawa 


A daren jiya Lahadi aka samu kifewar kwale kwale a karamar hukumar Auyo ta jihar Jigawa. 
Rundunar yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar haɗarin inda ta bayyana adadin mutanen da suka rasu. 
Legit ta tatttaro bayanan ne a cikin wani sako da kakakin rundunar yan sanda a jihar Jigawa, DSP Lawal Shiisu Adam ya wallafa a shafinsa na Facebook. 
Rundunar yan sandan jihar Jigawa ta bayyana cewa kifewar kwale kwalen ya jawo hasarar ran wata mata daya. 
'Yan sanda sun bayyana cewa akwai wata wata mata da ake nema tun jiya amma har yanzu ba a samu gano ta a cikin ruwan ba. Hadarin ya ritsa da yan kasuwa 20 ne cikin dare inda aka ceto 18 da ransu, daya ta mutu sannan ana neman daya har yanzu. 
Rundunar yan sanda ta bayyana cewa kwale kwalen ya kife ne sakamakon iska mai karfi da aka samu, rahoton Channels Television. 
An samu iska kuma matukin ya ɗibi mutane da suka wuce ƙima a dalilin haka ne ya gagara shawo kan kwale kwalen har ya kai ga kifewa. Har ila yau, kakakin rundunar yan sandan jihar, DSP Lawal Shiisu Adam ya gargadi al'umma kan yaɗa labaran da ba su da asali musamman a lokutan haɗura.