Haɗin Girkin BAKED YAM Dake Sanya Maza Santi
Haɗin Girkin BAKED YAM Dake Sanya Maza Santi
Kayan haɗi:
*Doya
*Attaruhu
*Albasa
*Gishiri
*Maggi
*Madara(ta gari)
Yadda za a haɗa;
*Da farko zaki samu doyarki mai kyau ki fere bayanta.
*Ki yanyanka ta ƙanana-ƙanana, sai ki wanke ta sosai.
*Ki zuba doyar a tukunya ki saka ɗan gishiri sai ki ɗora ta a wuta ta dahu.
*Bayan ta dahu sai ki sauke ta ki zube a kwando ta sha iska.
*Daga nan sai ki samo mazubi mai tsafta ki zube doyarki a ciki, ki saka jajjagen attaruhu kaɗan, yanda ba zai kama baki ba.
*Ki yi greating albasarki a abun goge kuɓewa sai ki juye ta akan haɗin.
*Ki zuba Maggi kaɗan (Ni dai da dunƙule ɗaya na yi amfani)
*Sai ki samo ƙaramin mazubi sosai ki dama madararki kaɗan ki zuba.
*Ki jujjuya sosai ko ina ya haɗe.
*Daga nan sai ki ɗauko bakin tray ɗinki da kika yi greasing ki shafe shi da butter, ki shimfiɗa baking paper a kai.
*Sai ki juye wannan haɗin naki a cikin tray ki gasa na minti 30-40.
Za'a iya ci da egg sauce ko Tea.
Enjoy it.
RUKY'S BAKERY
managarciya