Dalilin gabar da ke tsakanin ’yan Hausa Fim da Malaman Ahlus-Sunnah

Dalilin gabar da ke tsakanin ’yan Hausa Fim da Malaman Ahlus-Sunnah

Malaman Ahlus-Sunnah sun daɗe suna bayyana cewa fina-finan Hausa (Kannywood) suna ɗauke da abubuwan haramun kamar irin rawa, kiɗa, bayyana surar mata, haɗa maza da mata ba bisa ka’ida ba, da dai sauransu. 

Wannan ne yasa da dama daga cikin ’yan masana’antar Kannywood suka ɗauki Malaman Ahlus-Sunnah a matsayin masu tsangwamar sana'arsu ko masu hana kasuwancinsu tafiya.

Shekarun baya da suka wuce, manyan malamai na Ahlus-Sunnah sun yi ta huɗuba kai tsaye suna sukar masana’antar Kannywood da ’yan wasan kwaikwayo suna kiransu da yan iska masu lalata tarbiyya.

Dr. Idris Abdul-Aziz yana daga cikin manyan malaman Ahlus-Sunnah da ya dinga yin hudubobi da wa’azi yana caccakar yan Fim.

Ya rika bayyana cewa fina-finan Hausa suna lalata tarbiyya, suna koyar da alfasha da batsa, kuma suna gurbata tinanin matasa.

A wancan lokacin Imam Dr. Idris Abdul-Aziz Allah ya yi masa Rahama, ya kira masana’antar Kannywood da suna “maɓuɓɓugar alfasha” 

Dalilin da ya sa suka ɗauki Imam (Dr. Idris) a matsayin makiyinsu na kowa da kowa a cikin su.

Sai kuma rigimar hoton Rahama Sadau a shekarar 2020.

Lokacin da aka fitar da hoton Rahama Sadau tana rungume da wani jarumi na (Nollywood), Malamai da dama daga Ahlus-Sunnah sun yi tir da ita.

Malaman Alhlus-Sunnah sun rika yin wa’azi a masallatai su na kiran hakan wulakanci ga tarbiyyar Addinin Musulmi.

Kuma wannan gabar dake tsakanin Malaman Sunnah da yan FIM, ta samo asali ne saboda sun ce sana'arsu haramun ce, su kuma yan Fim suna ƙoƙarin kare haramtacciyar sana'arsu.

Saboda haka, masana’antar ta ɗauki malamai a matsayin barazana ga ci gabansu. 

Naxeer Kaoje