Yanda Za Ki Hada Romon Doya

Yanda Za Ki Hada Romon Doya
Romon Doya
Abubuwan da ake bukata:
Doya
Nama
Tattasai da albasa
Maggi
Oil
Curry's
 
 
Yanda zaki hada: 
Zaki yi slice doyanki ki wanke, Sai ki dafa nama tare da spicy,Sai ki yayyanka Naman kanana ki aje ruwan nama gefe Sai kiyi slice tattasai da albasa da tarugu idan kina bukata. 
Sai ki samu tukunya Mai fadi, Sai ki dauko doyan ki jera kasan tukunya, Sai ki dauko tattasai da kikayi slice da nama ki jera kan doyan, haka zakiyi tayi har ki jera su duka. 
Sai ki dauko ruwan Naman ki ki zuba, Sai ki saka maggi da curry's daidai yanda kike so. Sai ki rufe ki Dora kan wuta. 
Idan ya dahu Sai ki sauke Kuma kiyi a hankali wurin sakawa a cooler ko plate, kiyi amfani da cokalin suya kina daukowa daya bayan daya Sai ki zuba romon da shi zaki ci doyan. 
Safiya Usman