Sama da Mata 250 aka yiwa fyade a yankin Sakkwato ta Gabas--Honarabul Idris Muhammad Gobir

Sama da Mata 250 aka yiwa fyade a yankin Sakkwato ta Gabas--Honarabul Idris Muhammad Gobir

Honarabul Idris Muhammad Gobir tsohon shugaban karamar hukumar Sabon Birni mataimaki na musamman ga ministan 'yan sandan Nijeriya ya tattauna da Aminiya kan halin tsaron da yankin Sakkwato ta Gabas ke fama da shi don sanin yanayin da ake ciki.

Honarabul wani hali yankin Sakkwato ta gabas ke ciki kan halin tsaro kan yadda 'yan bindiga suka addabi yankin? 

Halin da yankin Sakkwato ta gabas yake ciki babu dadi, duk da yanda al'amurra suke na kai farmaki a wurin baki da ba su yankin za su ga ya ragu amma mu 'yan gida da mukasan in da mutanenmu suke da halin da suke ciki mun san ba dadi, a duk garin da yake yankin Sabon birni da suka gudu a garinsu ba wanda ya dawo, har yanzu da nake magana da da kai a wannan rana ta Talata ta wannan satin sai dai mutane suka baro garinsu, da marecen ma na hadu da mutane suna barin garuruwansu a tsakanin iyakar mu da karamar hukumar Goronyo.

Sakin wasu mutane da Bello Turji ya yi hakan ma wani abu bai canja ba?

 Ba abin da ya canja domin kafin Bello Turji ya saki wadan nan mutane ya yi hira da wani mai bincike kan aiyukkan 'yan ta'adda Dakta Murtala, ya fadi cewa ya tambayi Turji takarda da ke yawo kai ne ka rubuta ta ya ce shi ya rubuta takarda, ya tambaye shi saboda mi, ya ce saboda abuwan da ke faruwa suna sanya wanda bai ji bai gani ba ya fada ciki, don haka yake tausaya musu kan wannan al'amari kan haka yake son ya barsu. Ya fadawa Murtala anan wurin da nake ka ga in da aka kawo hari ya ce a'a, zaune yake a masallacin garin Dan Gwandi nan suka yi hirar, bisa dalilin tausayi ne ya sanya ya saki wadan nan mutanen 53, amma ba matsi na rashin abinci ko kai farmakin jami'an tsaro ba  har yau har gobe mun sanar da gwamnati ta yi abin da mutane suke so da yabawa shi yassa  muke fadar sabanin abin da ake fada mata wanda shi ne gaskiya domin mu ne ke wannan yankin ba dodon bango ba, a kullum 'yan bindiga ne ke kashe mutanen mu, ko jiya 'yan bindiga sun kashe Alhaji Arzika a garin Dan Kudan bangaren Burkusuma, sun tafi Gamji suna karbar kudi gida-gida suna yi wa mutane duka wanda ba a samu kudi ko wani abin kudi hannunsa ba, sun tafi Zangon Malam da Nasarawa da Ramalawa ma sun yi haka, duk abin da aka yi a gefen nan muna da shi rubuce ba shaci-fadi ba, mu ke da labarin nan domin kasar mu ce duk lungun da ake ta'adda mun sani don mutanenmu na fada muna, koyaushe ina Sabon Birni, duk wanda ba ya zuwa can karya yake yi ya ba da labarin gefen. Turji ya saki mutanen ba don wani matsi ba. 

A ina ne Kake ganin cikas kan yaki da 'yan ta'adda a yankin naku? 

Mu muna ganin duk abin da jami'an tsaro dake wannan fadan suke nema ana ba su domin ba mu taba jin sun koka ba kan hakkinsu, abin da yakamata dai su ji tsoron Allah kan wannan fadan, domin alamu na nuna wadan da ake sanyawa su yi wannan fadan ba su yin abin da aka tura su, mun yi ta fadin haka, tun da ake wannan  fadan 'yan ta'adda nawa aka kashe, shi ne ka sa ake zargin ba a tashi kawar da barayin ba, yanzu sai a rika fadin an samu sauki kamar yadda ake fadi, daga bakin Garin Gatawa zuwa Burkusuma a tsakanin akwai  gari 44 cikin garuruwan nan Gatawa ce kawai ke tsare da ka tsalka gulbin Gatawa za ka hadu da 'yan ta'adda gate ma gare su a wurin, a yau da nake magana da kai ba wanda ya isa ya shiga garin Magira, ba da amincewar 'yan bindiga ba, duk sun zageye garuruwan nan sun koma karkashin su, fada min saukin da aka samu, mu nasara a wurinmu a ce soja ya shiga Magira ya je Dama da Burkusuma tun da Fulanin nan na wurin duk wanda ka gani bangaren yana kiyo Bandits ne, in yau ka tafi da Saniya daya a Sabon Birni sai an karbe ta yau.

An zargi kun  Sanya siyasa a lamarin tsaro an kira ku taron tallafawa mutanen yankin  kun ki zuwa?

 Wannan taron bai shafi tsaro ba, mine ne kungiya za ta yi wanda ya shafi Sakkwato ta gabas, mutane su ke yin kungiya, kafin kafa wannan mi muka yi a gefenmu ai akwai kungiyar cigaban Gobirawa wadda tun bara mun hada kudi mun saye abinci na miliyoyin kudi mun taimakwa mutane da shi, mun hada kudi mun biyawa mutane kudin magani, mutanenmu daban-daban sun taimakawa mutane, Sardauna da Ibrahim Lamido da Aminu Boza da Shu'aibu Gwanda da 'yan majalisunmu duka sun ba da taimako, da sauransu, in ka ce maganar kungiya a yanzu baya fa? ita wannan kuniyar ta Sakkwato ta gabas cikinsu wane ne ke fadin abin da muka fada tsakani da Allah ga mutanenmu, ba maganar kungiya ake yi ba maganar mutane da kishin yanki ake yi.  Abin da ya sa ba mu zo a wurin taron ba tsarin da aka sanya wurin kaddamar da kungiyar siyasa ta shigo ciki, a wurin wani ya ce siyasa ce, a karshe Bafarawa ya nuna yana son Tambuwal ya yi shugaban kasar Nijeriya, in ya fadi haka ai ita ma APC tana da wadan da take son su yi shugaban kasar, fadin ana goyon bayan wani ai bata taro ne kuma wannan muka yi gudu, kuma in ka gayyaci  Aminu Waziri taron Sakkwato ta gabas domin yana gwamna mi zai hana ka gayyaci Ministan 'yan sanda Maigari Dingyadi, In ka kira mataimakin gwamna Manir Dan'iya mi ya hana ka gayyaci Ahmad Aliyu da yake sakataren asusun jindadin 'yan sanda na kasa, in ka gayyaci Ummarun Kwabo amatsayinsa na dattijo a jiha don mi ba za ka gayyaci Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ba, rashin kiransu mine ne wannan, mun fahimci wata manufa ce hakan ya sanya muka kaurace wa taronsu don in har cigaba ake so za a hada a tafi tare, Sanata Wamakko sau uku yana bayar da tallafinsa na shinkafa da gari da suga da tufafin sawa ga muatane  muna kai Sabon Birni, kuma kwamiti ke rabawa mutane wannan. Aje maganar siyasa a Sabon birni muna da kalubale irin wuraren Tagirke da Kiratawa da Darnawar Daji da Darnawar Mashekari har zuwa Tidibale a wannan yankin gari 23 ke wurin mace 250 aka yi wa fyade, ka tafi asibitin Sabon birni ka bincika ko yau(talata) an kawo wata yarinya mai shekara 10 da suka yiwa fyade an kawo ta a some jini na yi mata zuba a jiki, akwai wanda matarsa yau wata shidda bai sadu da ita ba kan yanda barayi suka yi mata kacakaca, da wasu 30 mazansu sun daina kwana da su har sai sun samu sauki, ga shi ba karfin da za su kai su asibitin jiha a yi masu gyara, suma yankin nan karkashin barayi suke, a garin Kimba ga fili suka tara mata suna yi masu fyade, da rana tsaka suka yi wa mata 34 fyade a cikin masallaci duk wani dan ta'adda mace biyu yake shiga da su masallaci a yankin kawai,  duk wuraren nan ba in da soja ya je, ka ce min akwai sauki.

Gwamnatin tarayya za ta fara aiki da jiragen yaki masu hadari kuna maraba da wannan aikin? 

Sosai kuwa duk in da jirgin nan zai yi aiki ba wanda zai tsaya matukar ba barawo ba ne domin akwai garuruwan da ba kowa a ciki, Gubutawa ba kowa bayan kashe mutum 12, Dandurumi ma bayan kashe 14, Gidan Madugu 3 da Gidan Makera 8 duk mun san wadan da aka kashe, ba kowa a wuraren. Muna maraba da duk wani abu da zai kawo mana karshen 'yan bindigar a wurarenmu, mun gaji gaskiya in har an tafi haka za mu dauki mataki na shari'a kan jininmu da dukiyarmu da ke salwanta a yankin, tun da ba mu gayawa mutanenmu su dauki makami an kasa kare rayuwarmu hakan kawai ya rage mana.