YADDA ZA KI HADA MIYAR ZOGALE TA MUSAMMAN

YADDA ZA KI HADA MIYAR ZOGALE TA MUSAMMAN
ZEZA'S CUISINE
 
 
 
 
 
Abubuwan hadawa
 
Zogale bushasshe
Nama
Maggi 5
Albasa 1
Attarugu 4
Gyada (dai dai misali)
Cittah
Tafarnuwa
Yadda ake hadawa
 
Da farko za ki wanke namanki kisa albasa da maggi ki dora a wuta ki tafasa
Sai ki gyara zogalenki ki ajiye a gefe ki jajjaga attarugu da albasa da tafarnuwa da cittah ki a jiye a gefe.
Sai ki duba namanki idan yayi saiki zuba jajageggen attarugun ki kara ruwa kisa maggi da gishiri dan kadan sai ki rufe yayi kamar minti biyar.
Idan yayi sai ki zuba zogalen kirufe yayi minti biyar shima sai ki zuba gyadarki ki rufe.
Idan ya nuna zakiji yana kamshi, sai ki sauke.
Ana iya cin miyar zogale da tuwo kowa iri.
 
 
 
 
(Zainab Muhammad jibril)
Zeza's cuisine
 
Enjoy
 
Share✅
Edit❌