Senata Iyorchia Ayuh PDP ta zaɓa sabon shugabanta

Farfesa Stella Effah-Attoe aka zaɓa shugabar mata da Hajara Wanka a matsayin mataimakiya. Muhammed Suleiman aka zaɓa matsayin shugaban matasa. Ibrahim Abdullahi kuma jami’in hulɗa da jama’a na Jam’iyyar, Honarabul Umar Bature Sakataren tsare-tsare.

Senata Iyorchia Ayuh PDP ta zaɓa sabon shugabanta


Jam’iyyar PDP ta zaɓi sabbin shugabanninta a babban taron da ta gudanar a Abuja.

Sanata Iyorchia Ayu ne aka zaɓa shugaban jam’iyyar a babban taron wanda ya zaɓi muƙamai 21 na shugabanni da za su jagoranci jam’iyyar ta adawa a Najeriya a zaɓen 2023.

Shugabannin sun ƙunshi jagororin PDP a sassan ƙasa.

An zaɓi wasu muƙaman ba hamayya, wasu muƙaman kuma mutum fiye da ɗaya suka yi takara a taron wanda aka fara a ranar Asabar zuwa Lahadi a dandalin Eagle Square Abuja.

An zaɓi Umar Damagum a matsayin mataimakin shugaban jam’iyyar PDP a shiyar arewa Taofeek Arapaja a matsayin mataimaki shiyar kudu.

Samuel Anyanwu ne sakataren jam’iyyar, yayin da aka zaɓi Ahmed Mohammed a matsayin ma’aji.

Farfesa Stella Effah-Attoe aka zaɓa shugabar mata da Hajara Wanka a matsayin mataimakiya.

Muhammed Suleiman aka zaɓa matsayin shugaban matasa. Ibrahim Abdullahi kuma jami’in hulɗa da jama’a na Jam’iyyar, Honarabul Umar Bature Sakataren tsare-tsare.
A muƙaman shugabannin gudanarwar jam'iyar an gudanar da su lafiya wata hatsaniyya.