Bambancin Ado Da Kwalliya a Tsakanin Maza Da Mata

Sai dai kwalliya da ake yi ta zamanin nan wasu abubuwa daga cikin kayan kwalliya suna cutarwa sai a kula sosai mata

Bambancin Ado Da Kwalliya a Tsakanin Maza Da Mata

ADO DA KWALLIYA
 
DAGA  INDIAN GIRL
 
 
Kwalliya ko kuma Ado duk da cewa dai suna da bambanci ita kwalliya mata ke yinta kuma ado
maza ke yinsa.
 
Misali za ka ji an ce ta caɓa kwalliya ko kuma ya caɓa Ado.
 
To ita dai kwalliya ko Ado abu ne mai matukar amfani sosai saboda suna kare kima da darajar dan adam musamman ma'aurata ana son mutum ya kasance mai yawan tsafta wato kwalliya ko kuma Ado tun ba
mata ba saboda su ne ma'abota kyale-kyale, don idan har ƴa mace bata kwalliya wani lokacin idan aka zo neman auren ta sai ka ji ana cewa ƙazama ce ko kwalliya bata iya ba, saɓanin maza sai dai ace masa ƙazami amma ba za'a ce kada a  aure shi ba.
 
 
Amfanin kwalliya ita kwalliya tana da amfani sosai ga ka ɗan daga cikin su:
 
1. Tana kawo kauna da kuma shauƙi tsakanin ma'aurata.
 
2. Tana tabbatar da kimar ƴa mace har da maza ma.
 
3. Tana ƙara tabbatar da siffan mutum da dai sauransu.
 
Sai dai kwalliya da ake yi ta zamanin nan wasu abubuwa daga cikin kayan kwalliya suna cutarwa sai a kula sosai mata.