Tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, wanda babban jigo ne a jam'iyar PDP, bai sami halarci babban gangamin taron jam'iyar na ƙasa ba ranar Asabar data gabata.
Premium Times ta yi rahoto cewa Jonathan ya bar Najeriya ranar Asabar domin halartar taron ƙungiyar Nahiyar Africa a Nairobi, Kenya, wanda za'a tattauna kan zaman lafiya a Africa.
Amma wasu ƙusoshin PDP na ganin tsohon shugaban ya yi amfani da wannan uzurin ne domin tsallake babban gangamin PDP.
"Idan har hankalinsa nakan taron, da kuma harkokin jam'iyya da ya halarci wurin na ɗan lokaci ya yi jawabi kafin ya wuce ranar Asabar din.
"Hakanan kuma zai iya turo tsohon mataimakinsa, Namadi Sambo, ko wani na kusa da shi, domin ya yi fatan alkairi a taron a madadinsa."
Wata majiya daga cikin PDP, ta bayyana cewa gwamnan Bayelsa, Douye Diri, da takwaransa na jihar Oyo, Seyi Makinde, sun gana da Jonathan ranar Jumu'a.
Majiyar ya ƙara da cewa lokacin zaman Jonathan ya faɗa musu zai tafi Nairobi, gwamnonin biyu sun bukaci ya halarci wurin taron na ƙanƙanin lokaci ya yi jawabi kafin ya tafi.
Hakanan gwamnonin sun masa tayin cewa za su shirya masa tafiyar da zai yi bayan an kammala taron, amma tsohon shugaban ya ƙi amincewa da shirinsu.
Hakan ya sanya mutane da dama na yin shagube da kallon kamar Jonathan ya fara neman yin wata tafiyar siyasa ba a jam'iyar PDP ba.
Ana ta rade-radin tsohon shugaban yana shirin komawa jam'iya mai mulki ta APC abin da wasu jagororin PDP ke karyatawa komine ne dai lokaci zai fitar da gaskiyar in da aka dosa kan tafiyar siyasar Jonathan.