DAY 30 @RAMADAN: YADDA ZA KI HAƊA MIYAR TAUSHE
BASAKKWACE'Z KITCHEN
DAY 30 @RAMADAN
MIYAR TAUSHE
INGREDIENTS
Alayahu
Nama
Kayan miya
Maggi
Gishiri
Kabewa
Manja ko mangyaɗa
Spices
Aunty na zaki yanka kabewar ki ƙanana ki wanke sai ki yanka nama ki wanke ki haɗa da kabewa da nama ki ɗora a wuta, su tafasa sosai yadda in kin sauke zaki iya latsa kabewar da ludayin miya ta ragargaje, to sai ki ɗaura manja yayi zafi yadda zaki soya nama da markaaɗɗen kayan miyan sama- sama sai ki zuba kabewa nan tare da su gishiri da maggi ,zaki zuba gishiri tun a tafashen nama, idan sun dahu zaki tsaida ruwa dai de yadda kike buƙatar kaurin sa sannan sai ki zuba alayyahu idan ya tafarfaso sosai sai ki sauke
zaki iya ci da waina, sinasir, fankasau, tuwo,alkubus etc
MRS BASAKKWACE
managarciya