Malamin addinin musulunci Malam Musa Lukuwa ya ki bin umarnin Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar ya gudanar da sallah karama tare da mabiyansa a wannan Lahadin sabanin Litinin.
A jiya Assabar Sarkin Musulmi ya sanar cewa watan Shawwal na wannan shekara ta 1443 bai kama ba.
Mabiya malamin sun gudanar da Sallar ne a birnin Sakkwato da karfe Takwas na safe.
A bayaninsa ga manema labarai Lukuwa ya ce ya samu cikakken rahoton ganin jinjirin watan a wasu wurare na Nijeriya da wajenta.
Ya kuma ce ba wata da'a ga kowa wurin saba ubangiji, "duk wanda ya yi azumi a yau ya yini ne da yunwar banza ba wanda ya sa shi domin wata azumi ya wuce" a cewarsa.
Al'ummar kasar Nijar sun yi sallah a yau Lahadi suma domin wata ya bayyanu a kasarsu.