Kamfanin BUA ya ba da tallafin karatu miliyan 40 ga dalibbai 200 na tsohuwar Sokoto

Kamfanin BUA ya ba da tallafin karatu miliyan 40 ga dalibbai 200 na tsohuwar Sokoto
 
 
Kamfanin samar da siminti na BUA ya bayar da tallafin karatu miliyan 40 ga dalibbai 200 dake manyan makarantu a jihohin tsohuwar jihar Sakkwato, domin ganin sun cimma burinsu a fannin ilmi.
Dalibban da suka ci gajiyar sun hada da matasa 50 daga Sakkwato, 50 daga Kebbi da 50 daga Zamfara, sai 50 a Wamakko in da gidan simintin yake da zama.
Kowane dalibi zai karbi naira dubu 200 an samu ninkin daliban kudin ma an samu kari da kashi 100 bisa ga shekarun baya.
Shugaba kuma daraktan kamfanin Injiniya Yusuf Binji ya ce sun ninka yawan dalibbai daga 100 zuwa 200 haka kudin daga dubu  100 zuwa 200.
Injiniya Binji ya bayyana tallafin karatun matsayin saka jari ne da zai samar da al'ummar mai ɗorawa a gaba.
Ya yi kira ga wadanda suka ci gajiyar su yi abin da ya dace kuma kamfani zai bibiyi karatunsu.
Shugaban kamfanin na BUA ya godewa gwamnatin jiha kan samar musu filin kasuwanci ba tsangwama.
Mai baiwa Gwamanan Sakkwato  shawara Honarabul Usman Arzika Fako ya ce tallafin zai bunkasa ilmi da samar da aikin yi ga matasa.
Ya ya bawa kamfanin ga wannan hobbasar akwai bukatar a duba wasu bangarori suma a yi abin da yakamata.
Balkisu Bello Muhammad daliba daga Kebbi ta bayyana BUA ginshiki ce ta samar da cigaba ta godewa kamfanin kan wannan saka jarin da suka yi da za su ci gajiyarsa a gaba.
Umar Bello dalibi daga Zamfara ya nuna farin cikinsa ga kamfanin yadda ya daga karatunsa zai samu nasara a gaba.