CONCOCTION RICE

 CONCOCTION RICE
BASAKKWACE'Z KITCHEN
 
 
 
 
     CONCOCTION RICE
 
 
INGREDIENTS
Rice
Dried fish, stock fish, crayfish, ice fish
Palm oil
Attarugu, Albasa, tafarnuwa, citta
Maggi, salt
Iru/daddawa
 
 
METHOD
Farko ki saka busassun kifin ki a cikin ruwa har sai sun yi laushi yanda zaki iya farfasawa sai ki wanke da kyau. Sai ki dauko crayfish ki sa daddawa kadan ki nika ko ki daka a turmi, ki tafasa shinkafar ki wanke.
 
Ki zuba busassun kifin a tukunya, sai ki zuba isashen albasa, ki murmusa maggi, da gishiri, sai ki zuba wanda zai dafasu suyi taushi, idan yayi, sai ki zuba dakakken tarugu da tafarnuwa, asa citta crayfish da manja, sai ki jujjuya, ki kara ruwa wanda zai isa ki karasa dafa shinkafarki, sai ki juye shinkafar ki jujjuya, ki kara ruwa idan bai isa ba, sai ki soya ice fish ki babbare ki cire 'kayar ki zuba a sama, idan ya nuna sai a sauke. Wannan ita muke cewa shinkafar manja a hausance. Amma wannan hadin special ne. 
 
 
MRSBASAKKWACE