Magoya bayan PSG sun yi wa Messi da Neymar gwalo da ihu

Magoya bayan PSG sun yi wa Messi da Neymar gwalo da ihu

Dubban magoya bayan Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta PSG, a yau Lahadi sun yi wa taurarin ƴan wasan kungiyar, Lionel Messi da Neymar gwalo da ihu kafin a take wasan kungiyar da za ta kara da Bordeaux a gasar Ligue 1.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa ihun ba zai rasa nasaba da fusata da magoya bayan su ka yi ba, bayan da Real Madrid ta cire PSG ɗin da ga Gasar Zakarun Turai a Larabar da ta gabata.

A wasan dai, PSG ce ke kan gaba, bayan da ta doke Madrid 1-0 a karawar farko, sannan da a ka zo karawa ta 2 a gidan Madrid, PSG ta sake jefa ƙwallo, amma da ga bisani Madrid ɗin ta farke ta ƙara kwakkaye 2.

Sakamakon wasan ya fusata magoya bayan PSG matuƙa, inda a yanzu haka, kafin fara wasan su da Bordeaux, sai filin wasan ya rude da ihu, da gwalo har da fito ga Messi da Neymar lokacin da su ka shigo cikin filin wasan.

Sai dai kuma da Kylian Mbappe ya fito, sai magoya bayan su ka riƙa tafa masa da kuma jinjina masa.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, PSG ɗin ta jefa wa Bordeaux ƙwallo 1 ta hannun Mbappe tun a minti na 24, inda yanzu haka tuni lokacin tafiya hutun rabin lokaci ya yi.