Sallah A Nijeriya Sai Ranar Litinin----Sarkin Musulmi

Sallah A Nijeriya Sai Ranar Litinin----Sarkin Musulmi

Kwamitin baiwa Sarkin Musulmi shawara kan harkokin addinin musulunci tare da kwamitin ganin wata na kasa ba su samu rahoton ganin watan Shawwal 1443 a ranar Assabar 29 ga watan Ramadan daidai da 30 ga Afirilu 2022.
Sanarwar wadda shugaban kwamitin kuma Wazirin Sakkwato Farfesa Sambo Wali Junaid ya sanyawa hannu ta nuna cewa za a cika Azumi zuwa 30 a gobe Lahadi..
Ya ce Sarkin Musulmi ya amince da rahoton da aka bayar don haka Sallah sai ranar Litinin 1 ga watan Sawwal.
Sarkin musulmi ya roki gafarar Allah a watan Ramadan da fatar samun zaman lafiya a kasar Nijeriya.