Yadda Za Ki Hada SAMOSA Na Musamman

Yadda Za Ki Hada SAMOSA Na Musamman
ZEZA'S CUISINE
 
 
 
                                                               SAMOSA 
 
 
Abubuwan hadawa
 
Fulawa (flour)
Kwai
Nama
Maggi
Onga
Kori (Curry)
Gishiri
Man gyada
Attarugu
Albasa
Karas (carrot)
Baking powder
Yadda ake hadawa
 
Da farko zaki wanke namanki ki tafasa shi da albasa da maggi da gishiri da dan korinki. Ki yi shi tamkar danbun nama.
Sai ki goga karas din ki, ki kuma soya shi
Sai ki zuba fulawarki a roba ki saka baking powder da dan gishiri ki kwaba. 
Ki murza ta murzu sosai ta yi fadi.
Sai ki rika yankawa kina zuba namanki da karas kina nadewa kamar dan kwali
Sai ki dora mangyadarki a wuta ya yi zafi
Idan yayi zafi sai ki dinga jefa nadadden samosanki kina kisoyashi
Ana baiwa maigida ya yaje da shi office, ko kuwa yara dan zuwa makaranta. 
 
 
zezas cuisine 
(Zeza's cuisine)
 
Zaku iya following dina a Instagram @ zeza's cuisine
 
 
Share✅✅