Buhari zai ƙaddamar da titin Zariya- Kano, sannan jirgi Air Nigeria zai fara tashi kafin a rantsar da Tinubu

Buhari zai ƙaddamar da titin Zariya- Kano, sannan jirgi Air Nigeria zai fara tashi kafin a rantsar da Tinubu

Ministan sufurin jiragen saman Najeriya Hadi Sirka ya tabbatar wa ƴan Najeriya cewa kamar yadda shugaban kasa yayi alƙawarin kafin wa’adin sa ya kare jirgin sama mallakin Najeriya zai fara tashi, ya na tabbatar da cewa hakan zai tabbata.

Sirika ya faɗi haka a lokacin da yake jawabi wa manema labarai a fadar gwamnati bayan taron FEC da aka yi na mako mako a fadar shugaban kasa.

Ministan ya ce an gama ɗiban ma’aikatan da zas u yi aiki da kuma du abinda ake buƙata, abinda ya rage shine amincewa Ƙungiyar kula da sufurin jiragen sama ta kasa da kaka, wato ICAO ta saka hannu a kai.

A karshe Sirika ya ce gwamnati ta amince a siyi na’irorin tantance murya da za a sassaka a tashoshin jiragen saman kasar nan 9.

Shi ma da yake nasa jawabin, ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed, ya bayyana cewa, titin kilomita 137 daga Kano zuwa Zariya da kuma kilomita 73 daga Zariya zuwa Kaduna, da kuma ayyukan gadar Neja na biyu za a mika su ga gwamnatin tarayya a ranar 15 ga watan Mayu domin kaddamar da su.

A cewar sa, titin Legas zuwa Ibadan mai tsawon kilomita 116 kuma za a mika wa gwamnati a ranar 30 ga Afrilu, yayin da aka kammala gadar Loko-Oweto da ta hada jihohin Nasarawa da Benuwai da gadar Utor a Delta.