Lokacin Siyasa Ya Wuce: Sakon Sarkin Sarkin Musulmi Ga Shugabanni A Nijeriya 

Lokacin Siyasa Ya Wuce: Sakon Sarkin Sarkin Musulmi Ga Shugabanni A Nijeriya 

 

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar, ya ja hankalin 'yan Najeriya game da abinda ya dace su maida hankali wajen yi wa sabbin shugabannin da aka rantsar. 

Sarkin musulmi  ya yi kira ga ɗaukacin 'yan Najeriya da su dage da yi wa sabbin shugabannin da aka rantsar addu'o'i kuma su mara musu baya don su kafa gwamnatin da zata amfani al'umma. 
Channels tv ta rahoto cewa Sarkin ya yi wannan kira ne a fadarsa da ke birnin Sakkwato jim kaɗan bayan dawowa daga sallar idi babba (Eid-El-Kabir) ranar Laraba, 28 ga watan Yuni, 2023. 
Bayan haka Sarkin Musulmin ya kuma ƙara kira ga hukumomin tsaro da su ƙara zage dantse su nunka kokarin da su ke wajen yaƙar 'yan ta'adda da sauran waɗanda suka hana zaman lafiya a kasar nan. 
Bugu da ƙari, Basaraken ya kuma roƙi sabbin shuwagabannin da suka karɓi ragamar ƙasar nan a matakai daban-daban cewa su rungumi kowa su yi aiki tare ba tare da duba banbancin siyasa ba. 
Alhaji Sa'ad Abubakar  ya faɗa wa shugabannin su tuna cewa lokacin siyasa ya wuce, yanzun lokacin jagoranci ne.