DA AURE NA: Labarin Yaudara Mai Muni, Fita Ta Biyu

DA AURE NA: Labarin Yaudara Mai Muni, Fita Ta Biyu
DA AURE NA,           *NA


     HAUWA'U SALISU (Haupha)Page 2 
Godiya ga My M K 
Cikin sauri ta fada wani gida, ta maido ƙofa ta rufe, ta cire hijab ɗinta ta faɗa ɗakinta ta kwanta saman kujera. Lumshe idanunta tai zuwa duniyar tunani.
"Tabbas ina matuqar daunarka Yusuf amma yazan da wannan jarabawa data sameni?
Anya ina da hankali kuwa dana fara sonka? Tabbas akwai tashin hankali sosai a gabana wanda bansan iyakar inda zai tsaya ba... 
Tib tib taji alamar shigowar mutum a falon tai masa kallo ɗaya ta maida kanta ta kwantas, saboda idan tana cikin tunanin Yusuf bata ƙaunar ko kaɗan taga gilmawai Amadu a idonta. 
Mintuna kaɗan ya fito ya sake gittawa ta gabanta ya fice, ta girgiza kanta ta koma tunanin hanyar da zata sake ganin Yusuf. 
Sallamarsa taji cikin matuƙar murna ta rufe eyes ɗinta alamar barci take tana jinsa ya ɗaga labulen ɗakin ya zuba mata ido yana murmushi,sake wata sallamai ya yi, amma taƙi motsawa, cikin tafiyarsa ta isa da taƙama ya shiga falon ya duƙo da fuskarsa daidai fuskarta yana jin yanda take fidda numfashinta, ya lumshe ido yasa hannu ya shafa fuskarta yai mata kiss a kumatunta, cike da shauƙi yace, "Ina matuƙar ƙaunarki wadda bansan sadda na afka cikin taba." ya sake shafa mata fuska yana ƙarema fuskarta kallo. Ita kuma taƙi buɗe idonta wai barci take da gaske. 
Murmushi ya yi "Nasan kina jina sai dai nima ba zan so kifarka ba don kada na daina ganin wannan kyakkyawar fuskar taki ba, domin sai naga kin fi kyau a hakan." Yana magana yana shafa fuskarta ahankali yana zagaye bakinta da yatsansa. 
Ganin ba zai daina ba ta buɗe idonta don tasan baƙaramin aikinsa bane yai abin da yafi hakanba.
Dariya yai mai ƙarama fuskarsa kyau yace, "Daman nasan ba barci kike ba dan naga fitarsa yanzu, ai baki isa yin barci ba kawai kina mun rowan ganin wannan idanuwan masu saukar da nishaɗi a gareni ne kawai."
Dariya tayi sosai wadda tasa ya saki baki da hanci yana kallonta ji yake tamkar ya rungume ta yadda dariyarta ke saukar masa da kasala a jiki, amma yasan bazata bari ba ko da yake zai jure akwai lokaci.
A hankali ta daina dariyar ta ɗauke hannunsa dake bisa cinyarta ta mike tsaye, taje wajen wani lungu ta ɗauko wata kula ta miƙa masa ba tare da tai magana ba. ɗan taɓe bakinsa yai "Kin san dai ba amsa zan ba sai idan tare zamu ci kuma yunwa nake ji sosai, amma ba zan ci ba tunda ban san ina kika samo shi ba."
Murmushi tayi ta bude kulan sai ga farar shinkafa da mai da yaji da maggi mai Star guda bisa kulan ta nuna ma shi tace "Ka gani sai ka ansa ko Malam? dariya yayi bazan amsa ba kije ki ɗauko cokali kizo mu ci don yunwa nake ji daman sosai." 
Kallon ka fiye rigima taimasa tace, "Kasan fa na ci nawa wannan naka ne ɗazun naso na faɗa ma muka rabu ba bankwana." 
Yatsine fuska ya yi "ke kika jiyo ni dai anji abin da nace, don haka in anso na ci aimun yanda nace, idan kuma bakiso to wallahi zan kwana da yunwa nasan za kiyi farin ciki ko?" Ya kalleta sosai yana son ya ji abin da zata ce. 
Kallon dai tai masa na ka fiye rigima ta aje kulan ta nufi wani ƙaramin ɗaki ta ɗauko cokali biyu ta dawo.
Dariya yasa mata "Kina nufin kowa da nasa wai? To baki isa ba da guda zamui amfani ni dake, sannan ke za ki ban nima na baki Indai kina son da gaske na ci abincin ga yunwa ina ji kin san ina da ulcer." Shiru tayi kanta a ƙasa tana jin rigimar da yake mata yau, kuma tasan ba zata iya barinsa da yunwa ba gara ace ta kwana bata ci ba daya kwana da yunwa saboda shi ne kawai ke sata farin ciki yazama dole itama ta sakashi koda bata son abin da ya sata ya zama tilas ta jure tai mashi. 
Kallonta kawai yake yana ƙara yaba kyan jikinta dan ba ƙarya Huwailat kyakykyawace ajin farko a cikin mata Allah Ya ba shi damar cika burinsa a kanta koda yake ba kowane namiji zai samu kamar Huwailat ya rabu da ita ba sai marai rabo, amma kuma ai ba a maraya sai raggo dan haka zai jure zai dake harya same ta cikin nuna jin haushi ya tashi ya nufi ƙofa bata san sanda ta jawo rigarsa ba ya dawo baya cikin maraicewa tace, "Please, karka tafi zan baka." Murmushi yai ya dawo ya zauna ya buɗe bakinsa. Dariya tayi ta girgiza kai "Baka gudun wani ya shigo ne?" kallon ko a jikina yai mata ahankali ta zuba masa abincin a bakinsa cikin taƙama yake cin abincin yana ta basarwa ya ciko cokali ya nufi bakinta bata da yanda zatai ta buɗe bakinta ya saka mata, a haka dai sukai ta cin abincin harya ƙare ta ba shi ruwa yasha .
Ya kalleta "Zanje wani waje ni da Abbas sai na dawo." Cikin shagwaɓa tace "Zance zaka je ko?" Dubanta ya yi yana murmushi yace, 
Haba wane zance za ni ina da kamarki? Ba zance bane, sai nadawo zan faɗa maki har bakin ƙofar gidan ta raka shi tana ɗaga masa hannu, shima yana ɗago mata har suka daina ganin juna ta koma ta haɗa kayan ta wanke.


Wacece Huwailat waye Yusuf waye Amadu?

Ku biyo Haupha dan jin wannan amsar 

Nagode 
07081095452