Mahaifiyar jarumin Kannywood, Ahmed S Nuhu ta rasu a ranar da ya cika shekaru 18 da rasuwa
Mahaifiyar jarumin masana'antar fina-finai ta Kannywood, marigayi Ahmed S Nuhu ta rasu.
Shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, Abba Al-Mustapha ne ya wallafa wannan labari a shafinsa na X a safiyar yau Laraba.
Ya ce ta rasu ne a daidai ranar da marigayi Ahmed ya ke cika shekaru 18 da komawa ga Mahaliccin sa.
"A daidai ranar da Abokinmu Marigayi AHMED S NUHU Yake çıka shekaru 18 da komawa ga Mahaliccinmu, ita kuma MAHAIFIYARSA Allah yayı mata rasuwa.
"Muna Addu’ar Allah ya jikan ta, ya gafarta mata Kurakuranta yasa Aljanna ce makomarta," in ji El-Mustapha.
Mu na addu'ar Allah Ya yi musu rahma, Ya kyauta namu zuwan.
managarciya