Gwamnatin Kaduna Ta Ƙaddamar Da Rusa Dubban Gidajen A Zariya
Rushewar ya biyo bayan kwashe shekaru ana tafka shari'a tsakin hukumar kwalejin da mazauna gidajen bisa dalilin kutsen haraba da kwalejin ke masu.
Gwamnatin Jihar Kaduna ta kaddamar da rusa dubban gidajen da ke bayan Kwalejin koyon tukin Jiragen sama NCAT da ke Zariya a yau Litinin.
Rushewar ya biyo bayan kwashe shekaru ana tafka shari'a tsakin hukumar kwalejin da mazauna gidajen bisa dalilin kutsen haraba da kwalejin ke masu.
Wasu masu gidaje da Aminiya ta zanta da su kan lamarin sun bayyana cewa suna rokon gwamnati da ta yi masu adalci na tallafawa.
Al'ummomin suyi kira da cewa su 'yan kasa ne ba bakiba kuma sunbi duk dokokin da ake bi kafin suyi gini a filayan san nan kuma dun bayyana cewa saye sukayi.
Aminiya ta ga yadda al'umma ke ta kwashe kayayyakinsu da kuma balle wasu daga cikin kayan rufin gidajen su da kansu
managarciya