CiwonBaya: Yadda za ka gane ciwon baya ya fara taɓa laka

CiwonBaya: Yadda za ka gane ciwon baya ya fara taɓa laka

Ciwon baya na daga cikin lalurorin da suke iya janyo shaƙe laka wanda kuma shaƙe lakar ke zuwa da matsalolin da suka fi ciwon bayan matsala.

Shaƙe laka a ciwon baya na iya kasancewa sababin bulli ko fashewar faifan tsakanin ƙashin baya wanda alamun shaƙe lakar sun fi bayyana nan take. Ko kuma shaƙe laka a ciwon baya sababin tsiro ko bunƙurowar ƙashin baya wanda alamun sun fi bayyana kaɗan da kaɗan.

A kowane yanayi dai, ana samun tsukewar kwararon laka wanda hakan zai janyo shaƙe laka, a wasu lokutan tare da jijiyoyin lakar.

Alamomin shaƙe laka sun haɗa da:

1. Ciwo a ƙasan gadon baya, wasu lokutan haɗi da ɗuwawu.

2. Ciwo mai farawa a ɗuwawu tare da sauka zuwa ƙafa da tafin sawu.

3. Jin nauyi ko saurin gajiya a ƙafa tare da jin ciwo mai damƙa a tsokokin ƙafa.

4. Jin dindiris, jin kamar ana tsira allura ko kamar shokin lantarki a ƙafa da tafin sawu.

5. Wahala ko ɗaukewar ji a fata, misali, idan aka shafa ko aka taɓa ko aka mintsini fatar ƙafar mutum sai ya ce ba ya ji.

6. Rauni ko rashin ƙwarin ƙafa da tafin sawu.

7. Ciwo mai ta'azzara da doguwar tsaiwa ko tafiya.

8. Matsalar saduwa da iyali.

9. Ƙwacewar fitsari ko bayan gida, idan shaƙe lakar ya ta'azzara.

Sau da yawa, ciwon baya yana farawa ne kaɗan da kaɗan, fara ciwon bayan na nufin wata matsala ta fara afkuwa a bayan kuma akwai bukatar ɗaukan mataki domin shawo kan matsalar tun da wuri.

Yin buris da ciwon baya ko kuma dogaro da shan maganin rage ciwo kullum tsawon lokaci na ƙara haɗarin ta'azzarar ciwon bayan zuwa shaƙe laka.

Ganin likitan fisiyo domin ciwon baya zai taimaka shawo kan matsalar daga tushe domin kauce wa haɗuran shan magani tsawon lokaci ko kuma tiyata daga ƙarshe.

© Physiotherapy Hausa