'Yan Sanda Sun Kama Matar Aure Data Kashe Mijinta A  Kebbi 

'Yan Sanda Sun Kama Matar Aure Data Kashe Mijinta A  Kebbi 

 

Hukumar yan sandan jihar Kebbi ta damke wata matar aure kan zargin kashe tsohon mijinta. Kakakin hukumar yan sandan jihar, SP Nafiu Abubakar, ya bayyana hakan a jawabin da ya fitar ranar Juma'a a Birnin Kebbi, birnin jihar, rahoton DailyNigeria. 

Ya ce sun damke matar ne daren Alhamis bayan samun labari daga wajen makwabta da suka ji ihu cikin dare. 
"A ranar 25 ga Agusta misalin karfe 11:40 na dare, jami'an 'yan sandan hedkwata Gwadan Gwaji sun samu labarin cewa an yi ihu daga gidan wani makwabci, Attahiru Ibrahim na Aliero quarters." 
"Yayinda muka samu labari, da wuri aka tura jami'an tsaro gidan kuma suka balla kofar gidan
"Sun tarar da Ibrahim kwace a kasa jina-jina kuma daga baya Likita ya tabbatar da mutuwarsa. 
"Hakazalika an ga Matarsa, Farida Abubuakar, cikin gidan." Kakakin yan sanda yace matar ake zargi da kisan mijin kuma an garkameta. 
Kwamishanan yan sandan jihar, Ahmed Magaji Kontagora, ya bada umurnin mayar da lamarin ofishin CID don bincike mai zurfi.