Ilmi da Kudi wane yafi dacewa Mace ta dauka a wurin zaben Miji?

Ilmi da Kudi wane yafi dacewa Mace ta dauka a wurin zaben Miji?

TSAKANIN ILMI DA KUDI WANE  YAFI DACEWA MACE TA DAUKA  A WURIN ZABEN MIJI?

 

Daga Saratu Zubairu

 
Mene ne ilimi? 

Masana sun bayyana ilimi a matsayin  a sanar da mutum wani abu a bisa hakikaninsa, wanda kafin hakan bai san shi ba, sanin ya zama  na hakika  ba na shakku da  rudu ba.

Shi ilmi baiwa ce da Allah  ke bayarwa ga bayinSa, shi ne gishirin rayuwa.

Mutum mai ilmi ya sha bamban da jahili ta kowace fuska, mai ilmi yana aiki ne ko barin aiki a sakamakon umarnin da ilminsa zai ba shi,  ilmin zai kasance tamkar shi ne linzamin da ke jan ragamar hankalinsa da al’amuransa. Da wahalar gaske ka samu lamurran mai ilmi sun baci domin yana da jagora a duk abun da zai aikata, zai bi tsari har abu ya kasance daidai ba tare da samun miskila ba. Ilmi haske ne da ke jagorantar mai shi ba zai fada cikin duhun kai da zai sanya shi neman mafita ba. Ilmi abun bukata  ne ga kowane mutum da yake numfashi, da shi ne ake bambance fari da baki, da sanin yakamata ko dacewar lamari. Girman ilmi ne ya sanya Allah ya baiwa Annabi Muhammad(S.A.W) ilmi. Komi da ka sani zai kare a duniyar nan ban da ilmi, duk wani ilmi da mutum yake da shi akwai sama da ilminsa. Ilmi ne kawai ba a karbewa, ba a gadonsa, baya gundura mai shi balle har ya zame masa kayan da yake son rabuwa da su.   

 Mine ne Kudi?  

Zamu iya fasalta kudi amatsayin sinadarin gudanar da lamurran yau da kullum, kudi na taka rawa ta bangaren al'amurran duniya ta hanyoyi daban-daban, wasu ma naganin cewa idan ba kudi rayuwa ba za ta yi dadi ba.

Muhimmanci kudi ne ya sanya kowane dan Adam na son ya mallake su. Addini da mutum yake yi yana tsayuwa ne in akwai kudi, rayuwa takan kara inganta da kudi a wannan zamani su ne ke jagorantar kowane lamarin duniya. Mai kudi ne kawai ke iya aikinsa ya kuma yi wa waninsa a lokaci daya a samu biyan bukata baki daya ba wani tangarda.

Kudi fa sun yi an samo su a rayuwar mutum mata da maza.  Duba da muhimmanci wadan nan ababen biyu ya sanya muka fitar da muhawara kansu wane ne yafi dacewa mace ta dauka azaben miji? 

 Halima Kadi ‘gaskiya aganina kudi sunfi ilimi saboda sai da su ake yin komai, ko ilimin ma sai da kudi ake nemansa.’ A cewarta. 

 Bashir Mukhatar “amsar wannan tambaya ai a fili take, ba za'a taba misalta ilimi da kudi ba, kudi na karewa amma ilimi ba zai taba karewa ba’ in ji shi.

 Mujitaba Bello  ‘gaskiya duba da yanayin da kasar nan ke ciki na rashi to kudi sun fi muhimmanci bisa ilimi, Za'a samu  ilimi ba kudi ne?  Kudi su ne jagorar lamurran duniya.’ A ta bakinsa.


Sadiya Zubair “ilimi yafi kudi, hujjata ita ce idan baka da ilimi ba za ka iya tafiyar da kudin ta hanyar da ta dace ba, duk kudinka idan baka da ilimi dole ne ka nemo mai ilimi” a cewar Sadiya.