'Yan Bindiga Sun Kashe Jami'an Tsaro 19 A Jihar Kebbi Yayin Ziyarar Mataimakin Gwamna
Daga Abbakar Aleeyu Anache.
Rahotanni daga jihar kebbi a arewa maso yammacin Najeriya na cewa yan bindiga sun kashe jami'an tsaro a kalla 19 a wani hari da suka kai a ƙauyen Kanya dake cikin karamar hukumar Danko Wasagu.
Maharan sun je ne kan babura a lokacin da mataimakin gwamnan kebbi ke ziyara a ƙauyen a ranar Talata,
Mataimakin gwamnan Samaila Yombe Dabai, ya shaida wa BBC cewa dakarun tsaron sun fafata ne da maharan amma bai fadi yawan jami'an da aka kashe ba,
Mutanen da suka mutu sun hada da Sojoji 13, da yan Sanda biyar da wani dan Sa-kai ɗaya.
Maharan sun kuma sace kayan abinci da dabbobi, masu yawan gaske,
Harin ya faru ne kwana daya bayan da 'yan bindiga suka kashe 'yan Sa-kai 63, yankin na Kebbi.
Matsalar ta addabi jihar a kwanannan ina da aka samu salwantar rayuwar mutane kusan 80 a cikin sati guda.
managarciya