Fatara Da Talauci Ni Iya Sanya ‘Yan Gudun Hijira Shiga Boko Haram----Zulum

Fatara Da Talauci Ni Iya Sanya ‘Yan Gudun Hijira Shiga Boko Haram----Zulum

Gwamna Jihar Borno, Babagana Zulum ya bayyana fargaba kan karancin kudi da fatara, idan ba a magance shi ba, na iya tilasta wasu mutanen da ke sansanin gudun hijira shiga Boko Haram ko ISWAP, rahoton Daily Trust.

Gwamnan, wanda ya bayyana hakan a jiya yayin rufe sansanin yan gudun hijira na Dalori-1, Dalori-2 Gubio da Muna a Maiduguri, ya ce gwamnati ba za ta iya cigaba da ajiye mutanenta a sansanin yan gudun hijirar ba.

Ya ce jihar, a karkashin jagorancinsa za ta yi duk mai yiwuwa domin ganin an mayar da mutane gidajensu cikin mutunci.

"Hanya guda da za a magance matsalar yan ta'adda shine gwamnati ta magance sillar abin wanda ya hada da karuwar talauci, rashin ababen cigaba da matsalar dumamar yanayi.

"Don haka, abin da ya kamata mu yi shine mayar da yan gudun hijira gidajensu cikin mutunci, Ba a tilasta wa kowa komawa gidansa ba, muna farin cikin tallafa musu komawa gidajensu bisa tsarin taron Kampala.

Za a tallafawa mutane da sana'a don su cigaba da rayuwarsu idan ba haka ba mutanen mu za su cigaba da zama a sansanin yan gudun hijira," in ji shi.