Ba Dalilin Daina Karɓar Tsoffin Kuɗi Bayan Doka Bata Hana Ba----Sanata Wamakko
Shugaban kwamitin tsaro na majalisar Dattawa ta ƙasa kana Sanata Mai wakiltar sokoto ta Arewa, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko Sarkin Yamman Sokoto ya yi kira ga Al'ummar Jihar sokoto da su ci gaba da Karbar tsoffi da sabbin Kudi tunda doka bata hana karbar su ba.
Sanata Wamakko ya yi wannan maganar ne yau Talata a Gidan sa dake Unguwar Gawon Nama sokoto Jim kadan bayan ya dawo daga Abuja wurin wani aiki na Musamman da ya shafi ci gaban Jihar sokoto.
Sanata Wamakko ya Kara da cewa, Jama'a na Kara matsar da kansu ne kawai idan suka ce ba za su Karbi kudin ba.
A bayanin da Bashar Abubakar Mataimaki na Musamman ga Sanata Aliyu Wamakko kan hulɗa da jama'a da manema labarai ya fitar ya ce ana kan tattaunawa ganin an shawo kan wannan matsalar saboda haka babu dalilin cewa ba a karbar kudin kuma ta ya za a ce mutum ya bada abin da bai da shi?
Ya ce sabbin kudin nan da ake magana kan su, babu su, to ya za a ce Kuma ba a karbar tsoffin?
Ya yi Godiya da irin hadin kan da ake ci gaba da baiwa ga wannan tafiyar ta Jam'iyyar APC a Jihar sokoto dama matakin kasa.
A ranar litinin ne Sakkwatawa suka fara fuskantar ƙarin matsala kan bankuna a jihar sun ƙi karɓar tsoffin kuɗi a hannun jama'a.
Gidajen Mai da shagunan kayan masarufi sun biye wannan sabgar in da kuɗi a hannun mutane suka zama tamkar takardar biredi.
managarciya