Ba za a yi zabe a cibiyoyi 240 ba a jihohi biyar na Najeriya--INEC
Join our subscribers list to get the latest news, updates and special offers directly in your inbox
Hukumar zabe ta Najeriya ta ce ba za a yi zabe a cibiyoyi kusan 240 ba a jihohi 28 a kasar lokacin zabukan da ke tafe, ranar 25 ga Fabarairu da kuma 11 ga watan Maris.
Shugaban hukumar, INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a yau Litinin lokacin da yake ganawar da ya saba da shugabannin jam'iyyu 18 masu rijista, a Abuja.
Shugaban ya ce dalilin hakan kuwa shi ne babu wani mai zabe da ya yi rijista a wadannan cibiyoyi 240.
Ya ce cibiyoyin da ba za a yi zaben ba suna jihohin Zamfara da Kwara da Edo da Rivers da kuma Imo wadda tafi yawansu da 38.
Farfesan ya ce bayan cibiyoyin 240 da ba za a yi zaben ba, duka sauran cibiyoyi kusan 176,606 a fadin kasar za a yi zabe.
Hukumar ta kuma yi gargadin cewa ba za ta amince da yanayin da jam'iyya daya za ta tura wakili fiye da daya ba a cibiyar zabe, su haddasa rudani ba, tana mai cewa duk wakilin da aka samu yana haka za a kama shi a gurfanar da shi gaban shari'a.
managarciya Oct 30, 2021 12 172
managarciya Feb 3, 2025 3 113
Maryamah Dec 14, 2021 2 90
managarciya Jun 24, 2023 5 77
Maryamah Dec 16, 2021 10 75
managarciya Nov 13, 2023 0 550
managarciya Nov 12, 2023 0 346
managarciya Nov 12, 2023 0 335
managarciya Nov 12, 2023 0 416
managarciya Nov 11, 2023 1 702
managarciya Nov 3, 2021 0 611
A wani hasashen an danganta samun ƙabilar Hausawa da auratayyar al’ummatai daga...
managarciya May 12, 2023 0 247
managarciya Dec 22, 2024 0 175
'Yan Najeriya sun san halin da suka tsintsi kansu bayan da BUHARI ya kifar da gwamnatin...